Ya Kamata A Shirya Taron Koli Kan Sha’anin Tsaro – Sheikh Musal Kasuyuni

- Advertisement -

Ya Kamata A Shirya Taron Koli Kan Sha’anin Tsaro – Sheikh Musal Kasuyuni

Daga Ibrahim A Muhammad

An bayyana matsalar tsaro da ake fama da shi a kasar nan da cewa ba inda ya fi tsanani irin bangaren Arewacin Nijeriya.

Sheik Musalkasuyuni Sheikh Nasiru Kabara ne ya bayyana hakan a wajen rufe karatun littafin Asshafa da yake gabatarwa a cikin watan Ramadan.

Ya ce yakamata a sami shirya taro na kololuwa wanda ake kira “Summit” da jagororin Nijeriya tun daga kan Gwamnoni zuwa kan sarakuna da manyan shehunai da manyan malamai zuwa kan manyan attajirai da yan siyasa.
Sheikh Musalkasuyuni Sheikh Nasiru Kabara yace yana bada shawara a sami wani taro dazai hada hada wadannan rukunan na Arewacin kasar nan su gamu a waje guda a karkashin ko mai alfarma Sarkin Musulmi ko kuma akwai wata Inuwa da ake gani a karkashinta ne za a yi wannan taro duk yanda dai aka ga ya fi dacewa a zauna a kalli hali da yanayin nan wanda Arewacin Nijeriya ake ciki.

Ya kara da cewa bala’i ya yi bala’i musiba ta yi musiba talauci ya ci karfin al’umma sannan ba a bar mutane solar ji zafi da radadin talauci da ya mamaye al’umma ba kuma an bi ana tusa fitinu iri-iri kuma ana ta bi ana karkashe al’umma.

Ya ce gabashin Arewacin Nijeriya abin da ya kama daga Borno,Yobe da abin da ya dangancesu  wannan bangare zuwa su Adamawa suna cikin tashin hankali suna cikin musiba a nan ma yammacin Arewacin Nijeriya abin da ya kama daga Zamfara, Sokoto , Kebbi, Katsina, Kaduna al’umma suna cikin tashin hankali.Neja itama yanzu wutar ta ruru ganga yana nema bala’in yana nema ya sport ko’ina.

Yace bala’i ya sport al’umma ya sport kasa an rasa maceci an rasa wanda zai kare .Abu biyu nan  su yake bada shawara da nasiha al’ummar Arewa ta kamasu a sahun farko addu’a a mataki na Biyu bayan addu’a sai an tashi an motsa anyi kazar-kazar anyi hobbasa to habbasannan ba wanda Allah ya dorawa cikin al’ummar Arewacin Nijeriya su tashi da wannan hobbasa da wannan yunkuri na nemawa al’umma mafita ta nemawa al’umma mafaka da matserata Kamar Gwamnoni da Sarakuna da manyan masu arziki, manyan Shehunai da Malamai na Arewa da manyan yan siyasa akwai wannan amanar a wuyansu.

Sheikh Musalkasuyuni yace yana fadar wannan ne a matsayin shawara amma a wuyar shugabanni ba shawara baee wajibin sune su tsaya suyi hakan kuma duk wanda bai tsaya a cikin su yayi rawar gani da Allah ya shedar ta cewa yayi iya kokarinsa ya kuma nemi haduwa da yan’uwansa akan su hadu su nemawa al’umma mafita daga wannan musiba da wannan bala’i ba a lahira sai Allah ya titsiyeshi ya tambayeshi akan wannan bala’i da bayinsa suka shiga suke fuskanta. Me ya yi duk gwamnoninmu da sarakunan mu sai Allah ya titsiye su ya tambayesu. Haka masu arziki da Malamai sai Allah ya titsiyesu ya yi musu wannan tambayar. Manyan ‘yan siyasa sai Allah ya titsiyesu ya yi musu wannan tambayar ai su ne shugabannin al’umma.
Ya ce abinda ake nufi da shugabanci shi ne a lokacinda wadanda ake shugabanta ake jagoranta suka shiga wani tashin hankali suka shiga wani kunci suka shiga takura da musiba a sannan shugabanci yake bayyana a sannan shugabanni suke nuna su shugaban 9 amma ba zasu amsa sunansu na jagorori ba a lokacinda al’ummarsu ta shiga cikin bala’i da musiba suka noke kowa yayi gum. Kowa ya tsaya kurum daga shi sai iya abinda ya shafe shi.

Sheikh Musalkasuyuni ya ce yana jiyewa shugabanni ko jagororin in suka cigaba da zura wa wannan lamari ido basu hada kai solar hada karfi waje guda ba solar samawa al’umma sa’ida solar sama musu mafita ba,yana jiye musu tsoron suma sai abin ya bisu gida-gida tun abin yana lamushe talakawa wallahi in basu tsaya sunyi abinda Allah yake nema suyi ba a hakkin wannan al’umma wallahi suma sai Allah ya cim musu a duk inda suke.Dan haka ya zama wajibi su tsaya suyi wannan aiki ko ba dan talakawa ba ko dan suma su tsira ya zama wajibi suyi.

Sheikh kasuyuni yayi addu’ar Allah ya yaye ya kawo mafita daga wannan masifu da bala’oi.

Ya ce al’ummar musulmi in suka gana da Ubangiji kar su bar wurin sai solar mika kuka da rokon Allah kan halinda al’umma ta shiga wannan bala’oi Allah ya tsayar dasu haka.Idan duk musulmin kasarnan zasu tssya kan addu’a baza ayi kwana 40 Ubangiji bai sauraremu ba haka al’adarsa ce amma sai an tsaya anyi da gaske in yaga gaskatarmu Ubangiji zai waiwayemu.

 

- Advertisement -