Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon

0
127

Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon

Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, wani tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya yi kira da a raba shugabancin da sauya shi tsakanin shiyyoyin siyasa shida na kasar.

Wannan, in ji shi, zai kasance mafi mahimmanci ga kwanciyar hankali da ci gaban kasar.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Gowon ba yin wannan bayanin ne a wajen bikin cikar kungiyar Tsoffin Dalian Makarantar Barewa (BOBA) shekaru 100 da kafuwa.

Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja [Goto]

A cewar rahoton, ya kuma bayar da shawarar da a samu mataimakan shugaban kasa guda biyu, daya daga yankin da shugaban ya fito sannan dayan kuma a kada mishi kuri’a a zabe shi zuwa karagar mulki yayin zaben shugaban kasa.

Ya kara da cewa: “Har ila yau, a tsakanin jihohi 19 na arewa ya kamata a sauya matsayin shugaban na Najeriya.”

Ya bayyana cewa babu wata kabila da ta fi kyau a wajen kasar kamar yadda take a matsayin Najeriya kasa daya dunkulalliya.

Gowon ya kuma ce matsayin gwamna a dukkan jihohin tarayyar ya kamata ya kasance a zagaye tsakanin gundumomi uku na sanatoci a kowace jiha, ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen rage nauyi da kuma kukan nuna wariya.

Ya nanata bukatar da ke akwai na kasancewar kasar nan dunkulalliya, yana mai cewa duk wani yunkuri na wargaza ikon ƙananan hukumomi ya kamata a ki shi.

A wani labarin daban, Doyin Okupe, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya nemi afuwa kan wasu maganganun da yayi a kan shugabancin Igbo a 2023.

Okupe, a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter ranar Asabar, ya ce ta hanyar yarjejjeniyar kasa ne kadai dan kabilar Ibo zai iya zama shugaban kasa a 2023.

Tsohon hadimin ya kara da cewa irin wannan matsaya ba za ta iya fitowa ba har sai babbar yankin arewa ta yafe wa Ibo a kan juyin mulkin 1966 wanda ya kai ga kashe Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.

What's On Your Mind?