Yaƙi tsakanin Boko Haram da ISWAP ya yi ‘ajalin ƴan ta’adda 54

0
209

Yaƙi tsakanin Boko Haram da ISWAP ya yi ‘ajalin ƴan ta’adda 54

kamar yadda jaridar bbchausa na ruwaito.Mayaƙan ISWAP da na Boko Haram ɓangaren Abubakar Shekau sun yi mummunan artabu da juna kan iko da wani yanki a Tafkin Chadi.

Jaridar PRNigeria ta ce ƴan ta’adda aƙalla 54 aka kashe a artabun tsakanin mayaƙan ISWAP da na Boko Haram ƴan ƙabilar Buduma a Jamhuriyyar Nijar.

A cewar jaridar ƴan Boko Haram daga ƙabilar Buduma suka fara kai wa ISWAP harin ba-zata a ƙauyen Chikka da ISWAP ke iko da shi a ranar 3 ga watan Maris domin kwasar ganima.

Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon

“Mayaƙan daga ɓangaren Shekau sun mamaye ƙauyen inda suka kashe ƴan ISWAP da dama tare da sace matansu guda biyar. Kuma mayaƙan sun saci kayayyakin abinci kafin su gudu a cikin dare.”

Daga baya kuma ISWAP ta kai harin ramuwar gayya inda suka yi ɓarin wuta da ƴan Boko Haram a yankin Kaduna Ruwa da Kaiga kuma an yi hasarar rayuka daga ɓangarorin biyu, a cewar jaridar.

Ubangiji Allah ya kara kunna wutar gaba a tsakanin su.

Source: bbchausa

What's On Your Mind?