Xi Ya Zanta Da Takwaransa Na Saliyo Ta Wayar Tarho

- Advertisement -

Xi Ya Zanta Da Takwaransa Na Saliyo Ta Wayar Tarho

Daga CRI Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na kasar Saliyo Julius Maada Bio ta wayar tarho.
Yayin zantawar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a shirya kasarsa ta ke ta karfafa hadin gwiwa da Saliyo a yaki da annobar cOVID-19, za kuma ta baiwa Saliyo taimako da goyon bayan a yakin da ta ke yi da wannan annoba.

A nasa jawabin shugaba Bio ya bayyana cewa, a shirye kasar Saliyo ta ke ta zurfafa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu, da karfafa alaka da Sin a fannonin ilimi, da lafiya, da samar da abinci.

A wannan rana kuma, shugaba Xi ya zanta da takwaransa na Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) Felix Tshisekedi da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Thomaa Bach.

(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

- Advertisement -