Xi Ya Aika Sakon Taya Murna Ga Bikin Baje Kolin Kayayyakin Sayayya Na Kasa Da Kasa Na Farko Na Kasar Sin

- Advertisement -

Xi Ya Aika Sakon Taya Murna Ga Bikin Baje Kolin Kayayyakin Sayayya Na Kasa Da Kasa Na Farko Na Kasar Sin

Daga  CRI Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika sakon taya murnar bude bikin baje kolin kayayyakin sayayya na kasa da kasa na farko na kasar Sin da aka bude a birnin Haiko na lardin Hainan. A cikin sakon nasa, Xi Jinping, ya yi nuni da cewa, shirya bikin baje kolin, ya ba da wata dama ta nuna kayayyaki da dandalin cinikayya, abin da ke zama wata dama ta baiwa dukkan kasashen duniya musayar damammaki a kasuwar kasar Sin, da damar farfadowa da ci gaban tattalin arzikin duniya. Xi ya ce, yana fatan dukkan kasashe da al’ummomi daga dukkan bangarori na rayuwa, za su yi aiki tare, ta yadda za su amfani al’ummomin dukkan kasashe.

A yau ne dai aka bude bikin baje kolin hajojin sayayya na farko na kasa da kasa na kasar Sin a birnin Haiko na lardin Hainan, inda masu baje koli kusan 1,500 daga ciki da wajen kasar Sin daga kasashe da yankuna 70 suka halarta.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

- Advertisement -