Xi Jinping Ya Yi Rangadin Aiki A Guangxi

0
185

Xi Jinping Ya Yi Rangadin Aiki A Guangxi

Daga CRI Hausa

A ranar 25 ga wata da secure, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Guangxi, inda ya ziyarci lambun tunawa da yakin kogin Xiangjiang a yayin doguwar tafiya da jar rundumar sojoji suka yi a shekarar 1934, a kokarin tunawa da mazan jiya masu juyin juya hali da gadon ruhin ‘yan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a garin Caiwan na gundumar Quanzhou da ke birnin Guilin. Sa’an nan ya je kauyen Maozhushan da ke garin Caiwan, inda ya yi rangadin wasu ayyukan farfado da yankunan karkara da tafiyar da harkokin kananan hukumomi.
A yammacin ranar 25 ga wata, Xi Jinping ya je bangaren kogin Lijiang a gundumar Yangshuo, don kara sanin yadda ake tafiyar da harkokin kogin da kiyaye muhallin halittu. (Tasallah Yuan)

What's On Your Mind?