Xi Jinping Ya Duba Aikin Sauya Hanyar Ruwa Daga Kudu Zuwa Arewa A Gundumar Xichuan Dake Birnin Nanyang

- Advertisement -

Xi Jinping Ya Duba Aikin Sauya Hanyar Ruwa Daga Kudu Zuwa Arewa A Gundumar Xichuan Dake Birnin Nanyang

Daga CRI Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping yana ci gaba da rangadin aiki da yake yi a birnin Nanyang, dake lardin Henan.

A yammaci jiya, shugaba Xi ya isa gundumar Xichuan, inda ya ziyarci wurin adana ruwa na Danjiangkou da kuma kauyen Zouzhuang, inda ya saurari bayanin gabatarwa sport da aiki da kula da yadda ake aiki sauya tsakiyar hanyar ruwa daga kudu zuwa arewa, da yadda ake kare muhallin wurin ake samun ruwa, ya kuma kara fahimtar yadda ake sake tsugunar da wadanda aikin ya shafa, da raya masana’antun wurin, da yadda ake inganta kudin shigar ’yan ci-rani.

A kan hanyarsa, Xi Jinping ya fita daga motar da yake ciki na nan wani lokaci, inda ya shiga wata gonar alkama don ganin yadda Alkama ta girma, aka kuma sanar da shi yadda ake noman hatsi a lokacin rani.

An dai raba aikin sauya hanyar ruwa daga kudu zuwa arewa ne gida uku: Gabas, da tsakiya da kuma yamma, inda za a rika jigilar ruwa daga kasa, tsakiya da kuma yankin saman kogin Yangtze zuwa bangaren arewa.

Tun a watan Oktoban shekarar 1952 ne dai, aka bullo da wannan gagarumin aiki. Yau shekaru bakwai da suka gabata ne, aka kammala hanyar gabashi da ta tsakiya na aikin sauya alakar ruwan daga kuda zuwa arewa, kuma wannan mafarki ya tabbata. Ya zuwa ranar 12 ga watan Disamban shekarar 2020, aikin layin tsakiya, ya yi jigilar ruwan da ya kai Kubic mita biliyan 34.eight, wanda ya amfani a kalla mutane miliyan 69. (Ibrahim Yaya)

- Advertisement -