Xi Da Putin Za Su Kalli Bikin Aza Harsashin Aikin Makamashin Nukuliyar Kasashen Biyu

- Advertisement -

Xi Da Putin Za Su Kalli Bikin Aza Harsashin Aikin Makamashin Nukuliyar Kasashen Biyu

Daga CRI Hausa

Gobe Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin za su halarci bikin aza harsashin aikin makamashin nukiliyar kasashen biyu ta kafar bidiyo.

Da yake Karin haske kan lamarin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, bikin shi ne na farko da shugabannin kasashen biyu za su gana ta kafar bidiyo a wannan shekara, kana a bana an cika shekaru 20 da kasashen biyu suka sanya hannu kan yarjejeniyar abokantaka, makwabataka da hadin gwiwa tsakaninsu Zhao ya kara da cewa, fannin makamashin nukiliya, wani dadadden bangare ne da kasashen biyu suke hadin gwiwa. Kana shugabannin kasashen biyu suna dora muhimmanci wajen bunkasa wannan fanni. (Ibrahim)

 

- Advertisement -