Xi Da Putin Sun Kalli Bikin Kaddamar Da Ayyukan Makamashin Nukiliya Tsakanin Kasashen Biyu

- Advertisement -

Xi Da Putin Sun Kalli Bikin Kaddamar Da Ayyukan Makamashin Nukiliya Tsakanin Kasashen Biyu

Daga CRI Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin suka halarci bikin aza harsashin aikin makamashin nukiliya tsakanin kasashen biyu, wanda ya gudana ta kafar bidiyo, inda suka yaba da hadin gwiwar kasashen biyu a wannan fanni.

An gudanar da bikin ne, domin shaida ranar farko ta gina kashi na 7 da na eight na tashar nukiliyar Tianwan da kuma tashar kashi na three da na four na tashar nukiliyar Xudapu.

A jawabinsa shugaba Xi ya nanata kudurin kasar Sin na kara dora muhimmanci kan alaka da kasar Rasha a fannin makamashi, saboda yadda kasashen biyu suka dade suna yin hadin gwiwa a kai.

Xi ya kuma yaba da yadda aka fara gina tashoshin nukiliyar guda biyu, yana mai cewa, ayyukan makamashi, solar kasance abin misali na kara yin hadin gwiwa a sauran fannoni tsakanin kasashen biyu.
Ya jaddada cewa, hadin gwiwar makamashin nukilya tsakanin kasashen biyu, yana da babbar ma’ana wajen raya hadin gwiwa bisa manya tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani. A don haka, shugaba Xi ya yi fatan sassan biyu, za su yi kokarin bunkasa hadin gwiwa a sauran fannoni.

Sin da Rasha solar kulla yarjejeniyar a watan Yunin shekarar 2018 dangane da gina wadannan sassan tashoshin nukiliya guda four cikin hadin gwiwa, wadanda babu kamarsu ya zuwa wannan lokaci, inda darajarsu ta kai sama da Yuan biliyan 20, kwatankwacin dalar Amurka biliyan three.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Rasha ta bayyana cewa, dukkan wadannan sassan tashoshin nukiliya guda four za su rika yin amfani da injuna samfurin VVER-1200 na zamani da kasar Rasha ta kera, maimakon injuna samfuran VVER-1000, sabbin nau’rorin solar dara su nesa ba kusa ba.

Da zarar ayyukan solar kammala, ana sa ran sassan tashoshin nukiliyar guda hudu, za su rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli. (Ibrahim)

- Advertisement -