Xi: Burin Juyin Juya Hali Ya Fi Kome Muhimmanci

0
78

Xi: Burin Juyin Juya Hali Ya Fi Kome Muhimmanci

Daga CRI Hausa

Tun bayan da aka kira babban taron wakilan JKS karo na 18, sai shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki a wurin da aka yi doguwar tafiya sau da dama, inda ya waiwayi doguwar tafiya wato Lengthy March, kuma ya tuna da doguwar tafiyar, hakika a cikin zuciyarsa, halin doguwar tafiyar ya riga ya shiga jinin al’ummar Sinawa, har ya kasance hali mafi muhimmanci na ‘yan JKS.

Sojojin kasar Sin solar jure wahalhalu masu yawan gaske solar kammala doguwar tafiya tsakanin watan Oktoban shekarar 1934 zuwa watan Oktoban shekarar 1935, a sakamakon haka JKS ta kaddamar da babban yunkurinta na tabbatar da ‘yancin kan al’umma da ‘yantar da al’ummar kasar.

Shugaban kolin kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, “Kila ne shan wahala zai rushe jikin mutum, ko kuma mutuwa za ta karbe ransa, amma ba zai yiyu ba a sauya burin ‘yan JKS, dalilin da ya sa aka yi nasarar kammala doguwar tafiyar shi ne, domin sojojin kasar solar doke abokan gaba, tare da warware daukacin matsaloli.”(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

What's On Your Mind?