Wuff ! Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa’ar mahaifiyarsa yayi murnar rabuwa da ita

0
51

Wuff ! Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa’ar mahaifiyarsa yayi murnar rabuwa da ita

Mawaki dan Najeriya, Usman Umar, wanda akafi sani da Soja Boy, ya jefa abin magana cikin jama’a yayinda ya caccaki tsohuwar matarsa, Lisa Hamme.

A bidiyon da ya daura a shafinsa na Instagram, Soja Boy ya bayyana yadda ya rabu da ita kuma yana godewa Allah da ya ‘yantar da shi daga hannunta.

Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un ! Mahaifin Jaruma Safiya Musa Ya Rasu

Legit nayi kokarin tattara wannan labari .Ya bayyana yadda mahaifiyarsa ta nuna rashin jin dadinda da auren mace sa’arta wacce ta girmeshi da shekaru 23.

Usman ya godewa Allah kuma yace da alamun asiri tayi masa.

Yace: “Ko dai an yaudarni ko kuma an yi mi asiri, kalli fuskar mahaifiyata da dan’uwana, gaba daya basu ji dadi ba amma a haka na cigaba. Na godewa mai sama da ya ‘yantar da ni.”

What's On Your Mind?