Watsi Da Tarbiyyar ‘Ya’ya Ya Kawo Tabarbarewar Tsaro A Nijeriya -Sheikh Jingir

- Advertisement -

Watsi Da Tarbiyyar ‘Ya’ya Ya Kawo Tabarbarewar Tsaro A Nijeriya -Sheikh Jingir

Daga Lawal Umar Tilde,

Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Izalatul Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah JIBWIS na kasa mai shelkwata a Jos, Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir, ne ya yi wannan kira a jawabin da ya gabatar alokacin rufe tafsirin da yake gudanarwa a masallacin yantaya Jos a makon nan da ya ce watsi da karantarwar Addinin Musulunci ne da al’ummar Musulmi suka yi ya sa ‘ya’yansu suka sami kansu cikin aikata munanan ayyuka.

Sheikh Jingir wanda ya ce tilas ne sai an koma an bi wannan hanya ta karantarwar Alkur’ani da Hadisi za a sami nasarar tsamo ‘ya’yammu daga cikin mummunan yanayi da su ka sami kansu na rashin tarbiya wanda yace a sakamakon haka yake sawa suke shiga kungiyoyin atsiri suna amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka.

Sheikh Jingir,  kuma ya ce Allah ya yi umrni ga iya ye da su shiga tarbiyantar da ‘ya’yansu karatun addini tun suna shekaru bakwai har sai solar kai shekaru 15 zuwa 27, sannan su barsu su cigaba da gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum ba tare da an jagorance su ba.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi su rika shiga cikin harkar siyasar kasar nan ana damawa da su ya ce mulkin dimukrdiyya na siyasa abu ne da ya ke tun tuni yake da asali kamar yadda Allah SWT ya bayyana a cikin Alkur’ani mai girma, saboda haka musulmi kada su yi kasa a gwiwa wajen zauwa yin rijista da zuwa jefa kuri’a.

Ya kuma yaba bisa yadda malaman da kungiyar ta tura tafsiri su guda 540 da masu ja masu baki guda 540 suka gudanar da tafsirin a jihohin kasar nan da kasashen waje kuma ya yi addu’a, wa Allah ya yafe wa biu daga cikin malaman da Allah ya yi wa rasuwa a cikin watan Azumi a wuraren da aka turasu yin tafsiransu.

Ya kuma yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Jihar Filato kuma shugaban gwamnonin jihohin Arewa 19, Rt Honarabul Simon Bako Lalong, bisa nasarorin da suka samu na inganta zaman lafiya da lumana a tsakanin al’ummar kasar nan.

Haka nan ya ya ba wa kokarin da kasar Saudi Arabiya ke yi don saukar da mahajjatan kasashen duniya a aikin hajin wannan shekara ta 2021. Kuma ya hori al’ummar musulmi das u cigaba da aiwatar da darusan da aka karantar da su a lokacin watan Azumin Ramadan da kuma yin wa shugabannin da kasa baki daya addu’o’in fatan akhairi.

- Advertisement -