Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Banka Wa Gidan Saurayinta Wuta A Binuwai

0
155

Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Banka Wa Gidan Saurayinta Wuta A Binuwai

Wata mata mai juna biyu ta bankawa gidan wani saurayinta wuta a yankin Achussa dake wajen Makurdi, babban birnin jihar Binuwai.

Wakilinmu wanda ya ziyarci wurin ranar Alhamis ya gano cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da rana, lokacin saurayin ya tafi wajen aikinsa.

Mazauna yankin solar ce tun da farko dai sai da matar ta tattara dukkan komatsanta daga gidan kafin daga bisani ta banka masa wutar tare da kone ilahirin kayan cikinsa.

Wani makwabcin yankin wanda ya bayyana sunansa da Joseph ya ce matar wacce ta kan ziyarci saurayin nata daga kauyensu a kai a kai, ta sha korafin cewa bai taba biya mata kudin motar komawa ba.

Gwamnatin Kano ta rushe gidan da masu garkuwa da mutane ke boye mutane

Hakan a cewarta ya sa a lokuta da dama ta kan dogara da ’yan uwanta ne wajen komawa gida, duk kuwa da cewa tana dauke da cikin da ya yi mata.

Joseph wanda bai iya hakikance asalin sunayen matar da saurayin nata ba ya ce ko ranar Talata sai da suka yi fada bayan ta bukaci ya bata kudin motar komawa amma ya yi kememe.

“Kashegari da protected sai ta bari sai da ya tafi aiki, ta fito dukkan kayanta sannan ta bankawa gidan nasa wuta. Sai dai ta yi rashin sa’a, makwabtan gidan solar cafketa kafin ta samu ta gudu.

“Nan take suka mika ta ga ’yan kato-da-gora, amma daga bisani bayan dawowar saurayin nata, sai suka roke shi da su sasanta lamarin ba tare da an je gaban ’yan sanda ba,” inji Joseph.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar ta Binuwai, DSP Catherine Anene, ta ce bata da masaniya a kan lamarin.

What's On Your Mind?