Wata Kungiyar APC Ta Nemi A Tsayar Da Matashi Shugabanci A 2023

0
65

Wata Kungiyar APC Ta Nemi A Tsayar Da Matashi Shugabanci A 2023

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

kungiyar APC Youth vanguard reshen jihar Neja ta nemi a tsayar da matashi takarar shugabancin kasar nan a zaben 2023, dan takarar shugabancin kasar kar ya kasa shekaru arba’in zuwa hamsin da haihuwa wanda kuma ya kamata ya fito a yankin arewa ta tsakiyar kasar.
Kodinetan kungiyar na jiha, Abubakar Mohammed Achis ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna fadar gwamnatin jihar, inda ya kara da cewar gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nuna sha’awarsa dan haka akwai bukatar a goya mai baya a wannan kudurin.
Ya bayyana cewar matasa sune mafi rinjaye a kasar nan kuma idan aka baiwa gwamna Yahaya Bello wannan damar kusan ya tabbatar da wakilcin matasa kashi saba’in ne na kasar.
Achis ya kara da cewar, maimaita zaben dan shekara sittin zuwa sama a zaben 2023 tamkar mayar da hannun agogo baya ne.
Ya bayyana cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan baiwa matasa damar neman irin wannan matsayin dan su yi anfani da hikima da basirar su a matsayinsu na matasa dan cigaban gwamnati.
Achis wanda matashin dan siyasa ne ya bayyana cewar arewa ta tsakiya itace yanki mafi zaman lafiya wadda ke bukatar duk mai son zaman lafiya ya shugabanci kasar nan saboda yankin na bada gudun mawa dari bisa dari tun a zabukan 1999 a zabukan shugaban kasa har yau ba ta canja ba.
Ya bayyana damuwarsa akan halin matsalar tsaron da ake ciki musamman halin da jihar Neja ke ciki, ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su hada kai wajen samun zaman lafiya, idan har yankunan karkaru ba su zaune lafiya ba wani cigaban da za a iya samu a siyasan ce.

What's On Your Mind?