Wata Kungiya Za Ta Shuka Itatuwa 10,000 A Yankin Abuja

0
128

Wata Kungiya Za Ta Shuka Itatuwa 10,000 A Yankin Abuja

Wata kungiya mai zaman kanta, mai suna ‘The Abuja GoGreen Mission’ ta sanar da cewa, ta samu nasarar shuka itatuwa fiye da 10,000 a kananan hukumomi 6 na yankin Abuja a cikin shekarar 2021.

Shugabar kungiyar, Mrs Aminat Aweke, ta sanar da haka a yayin kaddamar da shirin shuka itatuwan a makarantar gwamnati na GSTC da ke Garki a Abuja ranar Alhamis.
Ta ce, solar yanke shawarar shuka itatuwan ne don gyara muhalli tare da kuma maganin kwararowar Hamada a cikin kasa da kuma fuskantar dumamar yanayi.

Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta

Ta kuma kara da cewa, kungiyar ta shirya shuka fiye da itatuwa 100,000 a fadin tarayyar kasar nan, yayin da za ta tabbatar da shuka itatuwa fiye da 10,000 a yankin Abuja a cikin shekarar 2021.

“Maganar nan da muke yi da kai kungiyarmu na can na shuka itatuwa a jihohin Oyo, Lagos, Sokoto, Kano da kuma Kaduna, muna sa ran shuka itatuwa 10,000 a yankin Abuja daga cikin itatuwa 100,000 da muka shirya shukawa a fadin tarayyar kasar nan,” inji ta.
A jawabinsa,shugaban makarantar GSTC Garki, ya bayyana mahimmancin shuka itatuwa a wajen kare muhalli da kuma kara lafiyar al’umma

What's On Your Mind?