Wasu ‘yan bindiga sun kai hari Giwa jim kadan bayan harin sojoji akan abokansu

0
25

Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane da dama a kauyen Garawa, karamar hukumar Giwa jihar Kaduna.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da rundunar sojin sama ta samu nasarar kakkabe wasu yan bindiga a garuruwan Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.

Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Mr Samuel Aruwan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane da dama a kauyen Garawa, karamar hukumar Giwa jihar Kaduna

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da rundunar sojin sama ta samu nasarar kakkabe wasu yan bindiga a garuruwan Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.

Cikin Alhini Sadiya Kabala ta bayyana yadda sunka Rabu Da Jamilu Shinkafi Kafin yayi Hatsari Ya Rasu

Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Mr Samuel Aruwan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Aruwan ya bayyana cewa hukumar tsaro na ci gaba da bincike kan harin da aka kai Giwa, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a yankin.”

Aruwan ya bayyana cewa hukumar tsaro na ci gaba da bincike kan harin da aka kai Giwa, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a yankin.

Ya ce yan bindigar sun kai hari tare da kashe mutane biyu a wurare daban daban da ke a karamar hukumar.

A cewar sa, an kashe Alhaji Sa’adu a gundumar Fatika yayin da yan bindigar suka sace wasu mutane.

“Haka zalika, yan bindigar sun far wa kauyen Doka duk a cikin gundumar Fatika, inda suka yi garkuwa da wasu mutane.

“A kauyen Angwan Dan Yaya, a wannan gundumar, yan bindigar sun kashe wani mutum mai suna Alhaji Suleiman Audu.”

A baya Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya soki shugaba Muhammadu Buhari akan harkar tsaron ƙasar nan.

Mr Obasanjo, ya ce, abin takaici ne yadda shugaban kasa mai matsayin babban hafsan hafsoshin kasar nan ya gaza kawo karshen yan tayar da ƙayar baya.

Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan furuci ne jiya Lahadi da masanin tarihin nan, Toyin Falola, inda ya buƙaci shugaban ƙasa mai ci da ya farka daga dogon baccin da yake yi.

What's On Your Mind?