Wasu Na Shirya Makircin Kifar Da Gwamnatin Buhari – Femi Adesina

0
151

Wasu Na Shirya Makircin Kifar Da Gwamnatin Buhari – Femi Adesina

Daga Sulaiman Ibrahim

Mista Femi Adesina, mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai, ya yi zargin cewa wasu shugabannin addinai da Tsoffin ‘yan siyasa da suka gabata suna shirya makarkashiya don neman “tilasta canjin shugabanci da karfi ba ta hanyar dimokiradiyya ba” a kasar nan.

A wata sanarwa da ya fitar, Adesina ya ce a yanzu haka masu kulla makircin suna daukar shugabannin wasu kabilu da ‘yan siyasa, da nufin kiran wani irin taro, inda za a kada kuri’ar nuna rashin amincewa ga Shugaba Muhammadu Buhari, wanda hakan zai haifar da rikici a kasarmu Nijeriya.

Adesina, wanda ya bayyana irin wannan yunkuri a matsayin “haramtacce” da kuma “cin amana”, ya ce gwamnatin Buhari za ta ci gaba da hada kan ‘yan kasa da cigaban kasar.

Ya ce “Burinsu da suka kasa cikawa a akwatin zabe a zaben 2019, shi suke so su cika yanzun ta hanyar husuma “, yana mai gargadin cewa irin wannan shirin zai jawo a yankewa masu shirin hakan hukuncin da ya kamata.

Sanarwar ta fito kamar haka: “Ma’aikatar Harkokin tsaro ta cikin gida(DSS), a ranar Lahadin da ta gabata ta tsinkayar da mutane recreation da mummunan kokarin da wasu bata gari ke yi na yin barna ga gwamnati, da kokarin raba kan mutanen kasar nan.”

What's On Your Mind?