CULTISM: Wasu Matsafa Sun Watsa Wata Coci

0
37

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton matsafa ne an bayar da rahoton cewa solar harbi wani dattijo a lokacin da suka kai wani farmaki a kan wani Coci da ke kauyan Inen Ikot Esse a karamar hukumar OrukAnam ta Jihar Akwa Ibom.

Lamarin ya auku ne da jijjifin safiyar ranar Lahadi a lokacin da mutanan Cocin suke cikin gudanar da addu’o’in su, harin dai ya jefa firgici ga masu ibada a cikin Cocin da kowa ya watse yana neman mafaka.

Wasu Matsafa Sun Watsa Wata Coci

Wani da lamarin ya auku a kan idonsa mai suna, Sunday Ibanga ya ce, maharan wadanda yawansu ya kai kamar su 10 solar dirka Cocin ne da misalin karfe 7:05 na safiyar ranar , inda kuma kai tsaye suka nufi wajen da shugabannin Cocin suke gudanar da addu’o’insu kafin a fara addu’ar bakidaya a cikin Cocin.

Ibanga ya ce, solar harbi wani dattijo daga cikin shugabannin Cocin sau da yawa a kansa, inda suka bar shi a cikin jinni male-male, hakan ne kuma ya sanya sauran na cikin Cocin kowa ya ranta a na kare.

Ya ce a nan take Pasto din Cocin ya sanar da hedikwatar Cocin na su domin a kawo motar da za ta dauki wanda aka harba din zuwa Asibiti a nema masa magani.

Da take Magana daga Asibitin a ranar Litinin, matar wanda aka harba din mai suna Uwargida Iniobong, ta ce mijinta ya isa Cocin ne tun da sassafe domin ya gudanar da ayyukansa kamar yanda ya saba, ya bar ta a gida ita da sauran yara kafin su isko shi a can Cocin.

Ta ce a lokacin da suke shirin tafiya Cocin ne sai ta ji ana ta ihu a wajen kofar gidansu daga mutanan da suka zo da gudu domin su sanar da su cewa an harbi maigidan na su a lokacin da yake a wajen addu’a a cikin Cocin.
“Da aka shaida mani cewa an harbi mijina, sai na yi karfin hali na isa Cocin domin na dauko gawarsa na yi masa jana’iza. Amma sai na iske ‘yan sandan da suka taimaka mani na dauki mijin nawa zuwa Asibiti domin nema masa magani.

Bidiyo: Yadda Malami ke Yaƙi da Hare-Haren ‘Yan Ta’adda

“Tun daga jiya kawo yanzun, mijin nawa yana iya numfasawa ne kadai tare da taimakon injin numfashi a sashen bayar da taimakon gaggawa. Muna da bukatar kudi domin biyan gwaje-gwajen duk da aka yi masa kafin a yi masa tiyata domin a cire harsasan da suke a cikin kwakwalwarsa.

Ta ce lamarin ya auku ne a daidai lokacin da ake kan tattaunawa a tsakanin ‘yan kungiyar asiri na Debam da kuma na Iceland wadanda sam ba sa ga maciji da junansu a yankin, domin kawo karshen matsananciyar gabar da take a tsakaninsu da take zama barazana ga mazauna yankin.

“Wani da ya sadaukar da kansa ya shaida wa mani a lokacin da na ziyarci sansanin ‘yan kungiyar biyu, kuma duk solar musanta cewa suna da hannu a kan abin da ya faru na harbin mijina,” in ji ta.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ta Akwa Ibom, SP Odiko Mcdon ya ce, nan ba da jimawa ba rundunar za ta kama wadanda suka aikata wannan danyan aikin.

What's On Your Mind?