Wasika Zuwa Ga Marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’adua

0
178

Wasika Zuwa Ga Marigayi Malam Umaru Musa ‘Yar’adua

Bayan gaisuwa tare da fatan kana cikin dausayin rahamar ubangiji, Allah ya sa haka Amin.

A yau 5 ga watan Mayun shekarar 2021 ka ke cika shekaru 11 da amsa kiran mahaliccinmu. Tabbas ‘yan Nijeriya mun yi rashin nagartaccen shugaba, adali, mutum mai gaskiya da kokarin kamanta ta, shugaba masanin harkokin mulki da yin abin da ya kamata, shugaba mai ilimi da hangen nesa.

A yayin da nake rubuto maka wannan wasika idanuwa cike suke da hawaye masu zafi, ya yin da zuciya ta ke kuna da radadin irin halin da  kasar da kake kauna da son ganin ci gabanta, kasar da ka yi kokarin dorata a mizani na kwarai a lokacin rayuwar ka, sai dai kash yanzu kam ta dauko hanyar wargajewa, domin abubuwa solar tabarbare.

Narubuto maka wannan wasikar ne domin bayyana irin juyayi da halin zullumi, fargaba da zaman ɗar-ɗar da ‘yan Nijeriya musamman yankin Arewa suka tsinci kansu bayan rasuwarka, wannan yafarune sakamakon facali da akayi da kyawawan manufofinka.

Ko da yake nasan wasikata ba zata riske kaba, amma ina da yakinin za ta kai ga iyali da masoyanka masu kishi da son ci gaban kasar nan, wadanda suke maka addu’a ako da yaushe, kuma shakka babu addu’o’in mu zasu riske ka In Sha Allah, domin ka nuna mana kauna, ka kuma so ci gaban mu shi yasa zukatan mu ke ci gaba da begenka har yanzu.

Kamar yadda ‘yan Nijeriya za su yi maka shaida a ranar gobe kiyama akan yadda ka bijiro da kudurori guda bakwai (7), lokacin da ka hau kujerar shugabancin Nijeriya, wato (Seben Factors Agenda), wadanda ka bijiro da su da nufin kai kasar zuwa ga tudun mun tsira.

Kudurorin su ne:

Sai dai kash, an yi watsi da wadannan kudurori naka masu matukar alfanu bayan rasuwarka.

A yau an wayi gari yankin arewacin Najeriya musamman mahaifarka da jihar ka ta zama wato Katsina da Kaduna solar zamo sansanin ‘yan bindiga da ‘yan fashin daji, rayuwa ta zama babu tabbas a wadannan jihohi, manoma solar yi watsi da gonakinsu, ‘yan kasuwa masu safara solar hakura da yin safara saboda rashin tabbas akan lafiya da rayuwa, iyaye na fargabar tura ‘ya’yansu zuwa makaranta.

Kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula solar zamo ruwan dare a yankin arewacin Nijeriya lamarin da ya kai ga dawo da hannun agogo baya a dukkanin wata harka ta ci gaba, satar dalibai a makarantu ta zama tamkar ruwan dare, a kullum babu abin da kafafen yada labarai ke rawaitowa sport da jihar ka ta haihuwa sai an kashe mutane adadi kaza…, an kone gari kaza, an yi garkuwa da dalibai kaza da sauran abubuwa marasa jin dadi.

Allah ya sa kana Aljanna Firdausi Malam Umaru, yau an wayi gari yankin arewacin Nijeriya musamman jihohin Katsina da Kaduna da kuma Zamfara na kokarin zama kufai saboda matsalar tsaro da ta addabi yankin. Iyaye solar rasa ‘ya’yansu, Mata solar zama Zawarawa, ‘ya’ya solar zama marayu, kauyuka solar zama kufai sakamakon gudun hijira da al’umma ke yi saboda masifar rashin tsaro.

Allah ya kyauta makwancinka Malam Umaru Musa Yar’adua, hakika kazoo da kokarin inganta tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar samar da isasshiyar wutar lantarki, wanda hakan zai farfado da masana’antun ƙasar nan ‘yan kasa su samu ayyukanyi, inganta harkar sufuri ta hanyar samar da ingantattun hanyoyi, amma kash yanzu abin ba haka yake ba.

Domin a kullum harkar wutar lantarki a kasar nan kara ci baya take yi domin kullum kara zama a cikin duhu akeyi, hanyoyin mu solar zama tarkon mutuwa, saboda rashin kyawu da inganci.

Yau an wayi gari Nijeriyar da kake fatan ganin ta shiga cikin manyan kasashe irinsu Brazil da India wajen karfin tattalin arziki da ci gaba, yau tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa da addini da kabilanci da kuma rashin kwarewar masu jan ragamar mulkin kasar tana kokarin zama sansanin yaki.

A kullum rahotannin da ke fitowa daga yankuna daban-daban na kasar nan babu dadin ji, an kashe mutane kaza, an kone caji ofis din ‘yan sanda kaza, an kai hari gidan gwamnati kaza, an yi garkuwa da daliban makaranta kaza, an kashe jami’an ‘yan sanda ko Sojoji da sauran abubuwan da ke mayar da hannu agogo baya.

Labarin wasikar tawa cike take da bakin labarai masara dadin ji ga mu da muke raye a nan duniya, amma dai babban labari mai dadin ga reka shi ne, tabbas ‘yan Nijeriya za mu ci gaba da yin jimamin rasuwarka Malam Umaru Musa Yar’adua, musamman kasancewar ka gwamna da shugaban kasa na farko a Nijeriya da ka fara bayyana kadarorinka, da hakan ke kara tabbatar da kyamar ka ga cin hanci da rashawa a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya.

Da ana kiranye lallai da munyi maka, dama ance ba rabo da gwaniba…Kuma gashi muna tuna Bara, wanda hakan ke tabbatar da cewa ba muji dadin bana ba.

Amma zaka jinni da wani sabon labarin nan gaba idan wasu abubuwa solar sauya.

Ina fatan zaka ci gaba da kasancewa cikin salama da dausayin rahamar ubangiji.

Buhari Abba Rano, dan jarida ne kuma mataimakin mai bincike a Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci gaban Al’umma CITAD, Kano.

What's On Your Mind?