Wasan Chelsea Da Manchester City Zai Kayatar

- Advertisement -

Wasan Chelsea Da Manchester City Zai Kayatar

Tsohon dan wasan Manchester United da Manchester City, Owen Hargreabes, ya bayyana cewa wasan karshen da za’a fafata tsakanin Manchester City da Chelsea zai kayatar da masu kallo.

kungiyoyin kwallon kafa na Manchester City da Chelsea za su hadu da juna a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai da zai gudana ranar 29 ga watan nan a Istanbul, bayan nasararsu ta doke PSG da Actual Madrid.

A daren Laraba ne Chelsea ta yi nasarar yin waje da Actual Madrid daga gasar bayan zura mata kwallaye biyu da nema kari akan guda da ta zura mata a gidanta tun haduwarsu ta farko wadda aka tashi wasa daya da daya.

A bangare guda ita ma kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta yi nasarar kai wa wasan karshen ne bayan lallasa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta Faransa da kwallaye biyu da nema.

“Duka kungiyoyin solar cancanta su buga wasan karshe idan muka kalli yadda suka buga wasa a satin daya gabata saboda haka wasan da zasu buga zai bada mamaki kuma zai kayatar sosai yadda yakamata” in ji Owen Hargreabes
Wasan karshen dai zai zama kamar yadda ya gudana a shekarar 2019 lokacin da kungiyoyin firimiya na Liberpool da Tottenham suka hadu da juna, inda Liberpool ta yi nasarar doke Tottenham.
Tsakanin kungiyoyin biyu na Manchester City da Chelsea kowacce na ji da bajinta a wannan karon, bayan da kowacce ke ci gaba da nuna rawar gani a wannan kaka, inda Manchester City ke jagoranci teburin Firimiya ya yinda Chelsea ke matsayin ta hudu kuma taje wasan karshe na kofin kalubale.

Mai horar da kungiyar Manchester City dai ya yi ikirarin cewa rashin lashe kofin zai zame masa tamkar koma baya a tarihin horarwarsa ya yinda takwaransa na Chelsea Thomas Tuchel ke cewa lokaci ya yi da za su nuna Manchester City iyakarta.

- Advertisement -