Wannan Babbar Kasuwar Sayayya Ta Samar Da Dama Ta Cin Gajiya Ga Duk Duniya

- Advertisement -

Wannan Babbar Kasuwar Sayayya Ta Samar Da Dama Ta Cin Gajiya Ga Duk Duniya

Daga CRI Hausa

An rufe bikin baje kolin sayayya na kasa da kasa na farko na kasar Sin a jiya Litinin a lardin Hainan, kasar Sin. A cikin kwanaki four, kamfanoni 1,505, da samfurori dubu 2,628 daga kasashe da yankuna 70 solar halarci baje kolin, wanda kuma ya samu halarar mutane dubu 240. Baje kolin ya zama gaggarumin bikin sayayya na duk duniya.

Kididdigar da aka yi ta nuna cewa, daga cikin nau’ikan 2628 da suka halarci bikin bajen kolin, samfurorin kasashen waje solar kai kaso 51.9%. Ana iya cewa, karuwar karfin sayayya na Sinawa na kara samar da moriya ga kamfanonin sayayya na duniya.

Abun da ya fi mahimmanci shi ne, yanzu kasar Sin tana kokarin inganta bude kofa ga kasashen waje, don kara kafa makomar sayayya mai kyau a nan gaba. A hakika dai, lardin Hainan, inda aka gudanar da baje kolin, tashar jiragen ruwa ta cinikayya cikin ‘yanci ce da kasar Sin ke kokarin ginawa, bisa ma’aunin kasa da kasa.

A ranar da aka rufe bikin baje kolin, kamfanonin cikin gida da na waje guda 42, ciki har da L’Oréal, Parker, Deloitte, da sauransu, solar jagoranci sanya hannu kan yarjejeniya, kuma solar yi niyyar ci gaba da halartar baje kolin na biyu.

Ko shakka babu, wannan babbar kasuwar da ke kunshe da yawan al’umma fiye da biliyan 1.four, ta kasance dama da duniya baki daya ke iya cin gajiyarta. (Mai fassara: Bilkisu)

- Advertisement -