Wani Mutum Ya Kwashe Dan Makwabcinsa Da Ya Yi Garkuwa Da Shi A Kaduna

0
91

Wani Mutum Ya Kwashe Dan Makwabcinsa Da Ya Yi Garkuwa Da Shi A Kaduna

Daga Yusuf Shuaibu da Aliyu Usman Adam,

A cikin wannan makon ne wani saurayi mai suna Nazifi ya sace yaron makwabcisa mai suna Muhammed dan shekara shida a anguwan Badarawa da ke cikin garin Kaduna. Tun daga wannan lokaci iyaye da ‘yan’uwa da abokan arziki aka shiga jimami tare da rokon Allah ya bayyana shi.

Cikin ikon Allah sai wani makwakcin iyayen wannan yaro da tafiya ta kama shi zuwa Kano kwatsam sai ya ga wannan yaro(Muhammad) tare da wani mutumi mai suna Sani Galadima mazaunin Badarawa wadanda suke makwabta ne dukkansu. Sai wannan Bawan Allah ya dauki hotonsu tare ya aiko da hotunan gida tare da bayyana wa iyayen yaron halin da ake ciki. A daidai wannan lokaci iyaye yaron da masu garkuwa da mutanen da suka sace shi ana cinikin biyan kudin fansa, a inda aka biya su kudin fansan na naira milyan biyar.

Bayan an biya wadannan kudade, ba a sami Muhammad ba, hakan ta sanya aka kai rahoto ga jami’an tsaron farin kaya(SSS), inda suka tuhumi Sani Galadima wanda bayanai ke nuna cewa tsohon soja ne da aka kore sakamakon sata da yayi. Aka kama shi da bincike ya yi bincike ya bayyana yadda suka sace Muhammad da kuma wacce ta ajiye musu yaron a Kano. A cewarsa wani matashi mai suna Nazifi ne wanda yake makwabta yaron da aka sace(Muhammad) ya sato shi kuma ya kai ajiyarsa Kano. Shi kuma an ba shi naira dubu dari  takwas a matsayin nasa kason. Tare da tabbatar da cewa solar kashe Muhammad bisa dalilinsu na cewa ya gano fuskar Nazifi kasancewarsu suna makwabtaka da juna.

 

Galadima dai ya jagoranci jami’an tsaro har zuwa wajen da suka jefar da gawar Muhammad. An kuma dauko gawar da ta fara rubewa tana wari.

Wakilin MOBILIZED9JA YAU, Yusuf Shuaibu ya yi kokarin jin ta bakin mahaifin yaro, sai dai hakan ya ci turo. Amma duk da haka bai yi kasa a gwiwa ba ya samu nasarar zantawa da kanin mahaifin yaron mai suna Hassan Magayaki wanda ya bayyana cewa, wannan harka ce ta cin amana a tsakanin makwabtaka.

“Nazifi shi makwabci uban yaron ne na kusa wanda shi ne ya kira yaro a kan zai aike shi, ida daga wajen aikin ya bi shi ya tafi da shi zuwa Malali ya mika wajen Galadima.

“Daga nan ne Galadima ya tafi da shi zuwa Kano. Indsa daga nan ne aka fara ginikin kulin fansa tun daga miliyan 15 har aka dawo miliyan biyar. Inda aka kai musu naira miliyan biyar a Zaria da niyyar za su saki yaro da dare ko kuma da protected, saboda karamin yaro ne dole za su kawo shi wajen da za a ganshi.

“Sai dai ba mu ganshi ba da wannan daren har zuwa safiya, inda aka kira su a waya sai dai ba a samunsu.

“Asarin su ya tuni ne lokacin da wani daga cikin dan’uwa ya ga Galadima a tashar mota da ke Na’ibawa cikin garin Kano tare da wannan yaro sai ya dauki hotonsa a sirrance.

“Lokacin da Galadima ya koma gida sai aka kira jami’an tsaro suka kama shi. Idan binciken ya nuna cewa, lokacin da suka amshi kudin solar koma Kano suka kashe yaro saboda solar tambayi yaron ya gane su ya ce eh.

“Solar kashe yaron ne a cikin wani kwalbati, inda daya ya rike kafarsa, yayin da daya ya makure masa wuya har yam utu, sai suka jefa gawar a wannan kwalbati.

“Binciken ya sa ya bayyana kudin, inda ya dauko su daga cikin dakin matarsa tare da nuna wa mutanen gidansu. A yanzu haka dukkansu an sami nasarar kama su ciki har da yarinyar da ta ijiye yaron a Kano wanda ya kwana biyu a hannunta,” in ji kanun mahaifin yaron da aka kasha.

Kanin mahaifin yaro ya bayyana cewa, suna bukatar kamar yadda suka kashe wannan yaro to suma a kashe su.

Satar mutane da nufin amsar kudin fansa abu ne da ya yi kamari musamman yankin Arewacin Nijeriya, wanda a baya can sukan tare manyan hanyoyin ne su debi mutane su yi daji da su. Amma a yanzu kuwa abun ya dauki wani sabon salo inda ake hada baki da makwabta wasu ma ‘yan’uwa a sace wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Yana da kyau al’umma su kasance masu taka-tsantsan da kai komonsu tare kuma da addu’a. Allah ya kare.

 

What's On Your Mind?