Wane Salo Tuchel Zai Bullo Da Shi A Wasan Real Madrid Da Chelsea?

0
66

Wane Salo Tuchel Zai Bullo Da Shi A Wasan Real Madrid Da Chelsea?

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel na shirin amfani da wani salo a karawarsu da Real Madrid domin kange kyaftin din tawagar Sergio Ramos ba kuma tare da hada shi da wani dan wasa ba.

Tuchel wanda ya kware wajen sanya lamba tarar bogi a fili don karkatar da hankalin masu tsaron baya musamman a wasannin baya-bayan nan, ana ganin zai yi amfani da makamancin salon don raba hankalin masu tsaron bayan na Real Madrid, dai-dai lokacin da Chelsea ke fatan kai labari a karawar bayan tashi wasa 1 da 1 a haduwarsu ta farko a birnin Madrid satin daya gabata a Sipaniya.

A sakon da ya wallafa a shafinsa, Tuchel ya bayyana yadda ya ke yawan amfani da dan wasa Kai Habart wajen buga lamba 9 amma na bogi, wanda kuma ya na aiki matuka wajen karkatar da hankalin masu tsaron bayan.

Ramos wanda ya yi fama da jinyar da ta tilasta masa rasa haduwar farko, a wannan karon ne zai dawo wasa kuma ana ganin zai yi dukkan mai yiwuwa wajen taimakawa tawagar tasa ta hanyar hana zura  mata kwallaye a raga.

Publicité

Chelsea dai na kan ganiyarta ne a wannan kaka la’akari da irin nasarorin da ta ke samu a gasar Firimiyar Ingila, ko da Real Madrid ta yi kaurin suna wajen bayar da mamaki a gasar cin kofin zakarun Turai.

kungiyoyin Real Madrid da Chelsea dai solar tashi wasa 1-1 a karawar farko ta daf da kusa da karshe a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da suka kara ranar Talatar satin daya wuce a Spaniya.

A wasan na farko, minti hudu da fara wasan Chelsea ta ci kwallo ta hannun dan wasanta na gaba, Christian Pulisic, sai dai Real Madrid ta farke ta hannun dan wasanta na gaba, Karim Benzema tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Har ila yau, dan wasa Pulisic ya zama dan kasar Amurka na farko da ya ci kwallo a gasar cin kofin na zakarun turai na Champions League a daf da karshe, shi ne kuma matashin dan wasan Chelsea da ya zura kwallo a raga a gasar yana da shekara 22 da kwana 221 a duniya.

Shi kuwa dan wasa Karim Benzema, ya ci kwallo ta 71 a Champions League jumulla, hakan ya sa ya zama na hudu a jerin wadanda suka yi wannan bajintar tare da tsohon dan wasan kungiyar, Raul Gonzalez.

Wadanda ke gabansu solar hada da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo da kaftin din Barcelona, Lionel Messi da kuma dan wasan gaban Bayern Munchen, Robert Lewandowski.

Ranar Laraba 5 ga watan Mayu kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta kai ziyara filin wasa na Stamford Bridge dake babban birnin London domin buga wasa na biyu a Champions League.

Real Madrid ta lashe Champions League 13, Chelsea kuwa sau daya ta taba dauka shi ne a kakar wasa ta 2011 zuwa 2012 sai dai a wannan lokacin ana ganin kungiyar ta London za tayi iya yinta domin lashe kofin.

Bugu da kari, wannan shi ne karo na 30 da Real Madrid ta buga a wasan daf da karshe a Zakarun Turai, ita kuwa Chelsea ta yi na takwas ne sannan Real Madrid ta lashe guda 13 ya yinda Chelsea take da guda daya.

What's On Your Mind?