Wallahi zan shiga duniya idan ba a yi mun aure ba _ Inji Neenah

- Advertisement -

Ko da yake Ummi ta fito musanta sahihancin shafin da aka wallafa rubutun, amma jama’a da dama sun tafka muhawara game da rubutun nata.

Rubutun Matashiyar kamar yadda jaridar Dimokuraɗiyya ta gano, ya nuna cewa fa matashiyar a yanzu haka tana buƙatar aure ne, domin ta cika ta batse la’akari da abin da ta wallafa.

Ko da yake ba cikar ta auren ne ya janyo muharar ba, a’a sai dai irin katobara da take da shirin aikatawa idan iyayenta ba su mata auren ba, domin ta bayyana cewa a shirye take ta shiga duniya idan burin ta bai cika ba.

Ta wallafa cewa “A yi mun aure ko na lalace”

“Wallahi idan ba a yi mun aure ba zan kira ruwa ko na koma Lagos”

Kawo yanzu dai da Jaridar Dimokuradiyya ke hada wannan rahoto, ba ta samu ji daga bakin Matashiyar ba, domin wakilin Mu Bashir Khalid Furyam ya tura mata sako ta sahihin shafin da take ikirarin cewa shine na gasken, amma ba ta maida amsa.

- Advertisement -