Wake Ga Alan Waka Mai Taken ‘Daktan Waka’

0
49

An rubuta wakar nan ne, don taya Alhaji Aminuddin Ladan Abubakar (Alan waka), murnar karramarwar Dakta da a ka yi ma sa ranar Asabar, 26 ga Satumba, 2020.

Wake Ga Alan Waka Mai Taken ‘Daktan Waka’

Gun Daktan waka nake mika kyakkyawan fata*
Ya Alan waka, hazakarka ta sa fifita

Ga Daktan waka, kani, wanta, dangin babanta*
Madaurin aurenta, mai kai ta dakin angonta

Don GWADABE ka hau da ANGARA na san sai ka SHAHARA*
Har ATFAU nawa za ya zam ana saurarenta

Ka gama burge ni a JAMI’A ka rera BAKAN DABO*
Kai ne SARDAUNA a waka da zarar ka furta

A bar zancen FUJ’A a SAKARKARU da akwai tarke *
Tsaurin kalmomi ya KAMFA, ya atfa taushinta

KA MAYE amsa amo a MULUKIYA ya danka*
Mai jin FULFULDE da Chanis suna jin raujinta

Kai adu’ar UMMI MOMY ta zam LINZAMINKA*
Ka yi mana Alfiyya ta Rasulu Abba gun Binta

Kai Wa Zulum Hari: Adadin Wadanda A Ka Kashe Ya Karu

LU’ULU’U ka zamto da JAKADIYA ka bi sakonka*
Ka cika duk sassa na duniya cikinta da bayanta

Kai ne mai Sarki, da Sarki da Sarki, ba shakka*
Kai ma Sarki ne na waka da dukkan danginta

Aminu amintacce, fasihi, karimi, na sanka*
Tun a rubutunka na naso fasaha ga tsafta

Mai rauji, gunji, da amo da kyakkyawan tsari*
Kamusin Hausa, adabinta shi ne shaidata

HAGET photo voltaic ganoka, a yau Asabar suka ce Dakta*
Photo voltaic daga kimarka, amma a babin cancanta

Ya sanyo alheri Allah ya yi maka jagora*
Ya zam dafa’i, jalabi, a ko ina da ka je ka gifta

Naka Abulwarakat na Ayagi ni nay yo wakar*
Ina taya murna ne na kara da kyakkyawan fata

Zan disa aya nanba wakar gwani Daktan waka*
Don taya murna ne ga ALAnmu, ga wakar Dakta

Binyamin Zakari (Abul-warakat Ayagi),
26 ga Satumba, 2020

What's On Your Mind?