Wajibi Ne Mata Mu Hada Kai Mu Kuma Rike Mutuncin Mu- Dindey

- Advertisement -

Wajibi Ne Mata Mu Hada Kai Mu Kuma Rike Mutuncin Mu- Dindey

Hajiya Rukayya Mukaddas Dindey, uwa ce kuma jaruma a siyasa, wadda ta bada gudunmawar ganin jam’iyyar APC ta kafa mulki a jihar Neja. A tattaunawarta da Muhammad Awwal Umar, a Minna ta bayyana nasarorinta da kuma dalilin gazawar mata a tafiyar siyasa, wanda tace yana da nasaba da addini da al’adar inda mace ta fito.

Za mu so ki gabatar mana da kan ki ga masu karatun mu.

Da farko sunana Hajiya Rukayya Mukadas Dindey, Ni haifaffiyar Borgu ce kuma na taba yin aure yanzu haka ina da ‘yaya biyar, na yi karatu a kueens faculty kuma na kammala Gobt ladies science Secondry college da ke kuje Abuja.
Na cigaba da karatu domin samun diploma a jami’ar Usmanu dan Fodio Sokoto wadda ke da rashe kwalejin Ilimi ta Minna, na karanta psychology, a takaice ke nan.

Kasancewar ki uwar ‘yaya kuma sha’awar neman ilimi, me ya dauki hankalin ki na shiga siyasa.

Abinda ya dauki hankali na kuma ya ba ni sha’awar shiga siyasa shi ne ganin yadda ake hana mata fitar da muryar su a kasa baki daya, ba a daukkar mata, ana kallon ba za su iya shugabanci ba, wanda a tafiyar siyasar da mu ke ayau kuskure ne babba, ban da wannan akwai abubuwa da dama na hakkin mata ne da ya kamata a ce mace ke tafiyar da shi, domin su ne jagororin al’umma amma ana anfani da wani damar ana dan ne masu hakki.

Amma Allah cikin ikon sa bayan zuwan jam’iyyar APC a ragamar mulkin kasar nan, ana samun sauye sauye domin idan ka duba ban cin gwamnatin tarayya bisa jajircewar uwargidan shugaban kasa da ya baiwa mata damar samun mukamai da dama, ko a matakin jahohi solar taka rawar gani musamman jihar mu ta Neja.
Maman mu uwargidan gwamnan mu mai adalci, Dakta Amina Abubakar Bello ta taka rawar gani wajen janyo mata kusa da gwamnati, muna da kujerun kwamishinoni da mataimaka da masu baiwa gwamnati shawara da kujerun manyan daraktoci, kusan a wannan gwamnatin ce aka samu mace mai rike da kujerar shugabar ma’aikatan jiha da wasu mukaman da dama, ka ga ke nan zan iya cewar an fara samun sauyi a tafiyar da gwamnati wanda baiwa mata ire-iren wadannan mukaman yasa ake samun nasarar da ake gani yanzu, wanda muna fatar za a cigaba da irin wannan tafiyar.

Ya ki ke kallon irin yadda ake dan ne mata musamman idan an zo maganar takara da wasu muhimman abubuwa.
Kamar yadda na fada maka ne a baya irin matsalolin da mu ke samu duba da cewar kashi saba’in na masu jefa kuria lokacin siyasa mata ne, kuma su yi tsakanin su da Allah bisa amana da jajircewa, domin kuri’ar da mace daya za ta bayar, babu wani jinsin da ke ba da irin shi, dan suke shiga cikin gida wajen mata ‘yan uwansu Neman alfarma kuma dukkanin macen da ta amsa ta kan tabbatar har ‘yayanta da abokan zaman ta solar jefa kuri’a, amma daga baya idan an cin ma nasara su ake tauyewa a mayar baya, idan an samun dama yazo sai ayi watsi da su a dauko maza a ba su manyan mukamai, ka ga hakan shi yasa mata suke ta korafe korafen da ka ke jin suna yi.

Akwai mata ‘yan uwan ki a tafiyar siyasa da ke ganin lokaci yayi da ba wani dan takara ko a tafiyar jam’iyya ke da ra’ayin sai an yi yarjejeniya a rubuce kafin su marawa tafiyar siyasa. Ya ki ke kallon wannan salon.

Ni a nawa tunanin rakiyan dan takara ko tafiyar da jam’iyya ba wani abu ba ne da sai an rubuta yarjejeniya domin ko ka yi yarjajaniyar da shi yarjejeniyar da shi a rubuce ko ba kayi ba idan yana son ka da samu tabbas zai yi da kai, illa ‘yan siyasa su ji tsoron Allah su rika duba irin rawar da mu ke takawa a tafiya idan an samu nasara su rika ba mu damar da ta dace.
Yanzu muna ganin yarjejeniyar majalisar dunkin duniya ta fara tasiri domin mata mun fara rika kujerun shugabancin kasa wanda kowa ya ga irin rawar da mu ke takawa akwai cigaba sosai.

Amma ana ganin ba ku cika fitowa takarar kujerun da suke da girma ba, ko me yasa hakan
Dalilin shi ne ba mu da tabbacin idan mun fito za a mara mana baya, sannan kuma ita jamiyar da kan ta ba ta baiwa mata goyon baya lokacin da suka yunkuro da zancen takara, na biyu kuma shi ne akwai dalilai na addini, da yanayi yanki da macen ta fito, babban dalili shi ne rashin samun goyon baya na kudaden da ake kashewa lokacin yakin neman zabe.

Kamar ke ma kina da mukami a gwamnatin jiha, kina ganin za ki yi anfani da wannan damar dan yin takara a zaben 2023 mai zuwa
Lallai ina rike da mukami a wannan gwamnatin ta Alhaji Abubakar Sani Bello kuma yana yabawa da irin rawar da ni ke takawa. Amma batun takarar 2023 na mai yawancin rai ne. Amma dai tafiyar yanzu muka fara ta, za mu cigaba da yardar Allah idan da numfashi.

Jihar Neja na daya daga cikin jahohin da ke fuskantar matsalar tsaro, ya ki ke kallon rawar da gwamna ke takawa
Hakikanin gaskiya zancen tsaro a jihar nan, gwamnatin na bakin kokarinta, amma kasan matsalar sai in ce kamar duka duniya ce, domin batun rashin samun kwararar tsaro ya zama ruwan dare. Duk kokarin da gwamnati ke yi akan ta ga hakan ya saukaka duk a banza ne saboda akwai masu labewa suna yi mata zagon kasa, muna dai fatan Allah ya kawo mana karshen sa da masu ganin sai solar ruguza kasar.

Dakta Abubakar Sadik Sani Bello dai a fanin tsaro da saura kam. Saboda duk yadda aka iya tunka wasu na nan da Allah shi ya san su suna warware tunkan. Muna fata Allah ya masa jagora ne abun ya kawo karshe kafin wa’adin gwamnatin mu ya kare.

Wani shawara za ki baiwa mata ‘yan uwanki.

Shawara ta ga mata ‘yan uwana shi ne mu kama kanmu, mu nuna wa duniya cewar hadin kanmu shi ne zai kawo mana cigaba da samun yadda mu ke so. Mu Kuma fito ayi ta fafutukar siyasar da mu musamman daga karkaran da muka fito mu tabbatar mun dunkule waje daya ba a iya fasa mu ba.

Kin fito daga gundumar Bussa, me za ki shaidawa mutanen ki a wannan tafiyar
Mutanen Bussa ina shaida masu cewar idan suka ba mata damar fitowa takara lallai za su ga canji in Allah ya yadda dan mun san matsalolin da ke damun al’ummar mu. Domin kusan rashin cancanta da dacewar ‘yan takarar da mu ke tsayarwa shi yasa kullun mu ke a waje daya.

Honorable, muna godiya da lokacin da ki ka ba mu
Ina godiya, Allah ya kara daukaka ku ya kuma cigaba da baku kwarin gwiwa.

- Advertisement -