WAEC Ta Rike Sakamakon Jarrabawar Dalibai 215,149

Hukumar shirya jarrabawar fita daga makarantun sakandare ta Yammacin Afrika, WAEC, ta fada a jiya Litinin cewa, ta rike sakamakon jarrabawar dalibai 215,149, wadanda su ka rubuta a wannan shekarar ta 2020 a Nijeriya.

Hukumar ta WAEC ta ce sakamakon jarrabawar da ya yi daidai da kashi 13.98 na jimillar daliban da su ka rubuta jarrabawar, hukumar ta ce ta na rike ne da shi a bisa zargin su da aikata almundahana.

WAEC Ta Rike Sakamakon Jarrabawar Dalibai 215,149Patrick Areghan, shugaban sashen na WAEC a Nijeriya, wanda ya bayyana labarin hakan ne a Legos, a jiya da safe a lokacin da ya ke shelanta sakamakon jarabawar bakidayansa.

Bidiyo: Kukan Rahama Sadau wasan kwaikwayo kika yi mana dama kin saba kuka a finafinai

A cewarsa, a na kan bincikar rahotannin aikata almundahanar kuma nan ba da jimawa ne ba za a gabatarwa da kwamiti sakamakon binciken domin tantancewa da kuma daukan matakin da ya dace.

Ya kara da cewa; jimillan dalibai 81,718 wadanda ya yi daidai da kashi 5.31 akwai wasu darussan su da a ke kan tantancewa a sabili da wasu kura-kurai daga su daliban. Amma a na kokarin ganin an hanzarta kammala gyaransu ta yadda daliban za su sami sakamakonsu a kan lokaci.

 231 total views,  1 views today

About M. Jamiu 1389 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*