MUSIC + VIDEO: Wa’azi Akan POS Mai tayar Da Hankali – Sheikh Abubakar Mukhtar Yelwa

0
106

A jiya na saurari fatawa akan kasuwancin da matasanmu sukeyi da na’urar POS wanda babban Malaminmu, Sheikh Abubakar Mukhtar Yola yayi.

Mallam a bayaninsa wanda yake cike da hujjoji ya tabbatar da cewa kasuwancin da akeyi da na’urar POS saboda cire kudi da kuma bawa mai na’urar wani kaso na kari akan abunda mutum yake bukata HARAMUN NE a musulunci saboda riba ne.

Wannan wa’azi ya tayarmin da hankali saboda dalilai guda biyu, na farko, ina cikin mutanen da suke ta’ammuli da wannan hanyar ta kasuwanci wajen cire kudi nayi bukatuna, na biyu ganin yanda matasanmu suka rike wannan hanya a matsayin sana’a.

Wa’azi Akan POS Mai tayar Da Hankali - Sheikh Abubakar Mukhtar Yelwa

Mallam yana cikin mutanen da ganinsu kawai idan nayi yakan sani na tuna Allah, wannnan fatawa kuma na dauke ta da muhimmanci har sai nasamu wanda tafita kwararan hujjoji. Idan ba lalura ba, insha Allah mundaina daga yau.

Wanda mukayi akan rashin sani Allah ta’ala ya yafemana.

DOWNLOAD VIDEO

What's On Your Mind?