Uwar Gidan Gwamnan Katsina Ta Nemi A Kara Kaimi Wajen Samar Wa Yara Abinci Mai Gina Jiki

0
104

Uwar Gidan Gwamnan Katsina Ta Nemi A Kara Kaimi Wajen Samar Wa Yara Abinci Mai Gina Jiki

Daga Maigari Abdulrahman,

Matar Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Masari, ta yi kira ga masu hannu da shuni da su kara kaimi wurin zakulo musabbabin karuwar mastalar abinci mai gina jiki da kuma mutuwar yara kanana a jihar.

Ta yi kiran ne a ranar Alhamis a wani taron manema labarai kan matsalar yara masu fama da ciwonrashin abinci mai gina jiki jiki a jihar.

Ta bayyana cewar, matsalar abinci mai gina jiki ga yara na dai daga cikin musabbabin yawaitar mutuwar yara kanana, wanda hakan ke hana su girma zuwa shekarun samartaka.

“ Ina roko ga dukkan masu hannu da shuni da a hada hannu da karfe wurin ganin an ceto yaran da ke fama da matsalar, da kuma hana salwantar rayuwarsu.”

“Masana solar yi bayanin cewar, martsalar garkuwar jiki na da illa ga yara, tana raunata kwakwalwar yara wanda hakan ke illata hazakar su a makaranta,” in ji ta.

Ta cigaba da cewa, “Dukkan abinda za a yi a wani banagaren, to rashin kula da yara cikas ne ga cigaban jiha dama kasa bakidaya. Yanzu muke da damar yin abinda ya dace da kuma gyara gobenmu”.

Da take kara yin kira ga wadanda abin ya shafa, ta ce akwai bukatar kowa ya sauke nauyin da ya hau kansa domin ceton rayuwar yaran. A bayanin ta, ingantattar shayarwa na dai daga cikin hanyoyin rigakafin kamuwa da matsalar abinci mai gina jiki ga yara.

Iyaye mu tsayu da namu bangarem, maza kuma su tsayu da bada tasu  gudunmawa da tallafawa yanda yakamata, gwamnati ma ta kaira kaimi da bayar da muhimmanci kan fanni, ta roka.

A  nata jawabin, mataimakiyar Darakta ta hukumar ayukkan asibiti, Dakta Uwani Muhammad, ta ce kaso 50 na mutuwar yara sakamakon rashin abinci mai gina jiki ne.

What's On Your Mind?