Uwa ta yi wa ‘ya’yanta yankan rago saboda kishiya in Kano

0
202

Wata matar aure mai suna Hauwa da ke zama a kwatas ta Diso da ke karamar hukumar Gwale ta jihar Kano ana zarginta da yi wa ‘ya’yanta biyu yankan rago.

Hakan ta faru bayan rikicin da ya auku tsakaninta da mijinta mai suna Ibrahim Haruna Aminu wanda bai dade da yin sabuwar amarya ba.

Jaridar Solacebase ta wallafa cewa, yaran da mahaifiyarsu ta yi wa yankan ragon su ne Yusuf Ibrahim mai shekaru 5 da kanwarsa Zahra’u mai shekaru uku.

Wani kawun yaran, Sadiq Haruna Aminu, ya ce Hauwau wacce matar dan uwansa ce kuma mahaifiyar yaran, tana rayuwa cike da hassada da kishi tun bayan da dan uwansa ya auro wata matar, lamarin da yasa ta kashe ‘ya’yanta biyu a ranar Asabar.

Uwa ta yi wa 'ya'yanta yankan rago saboda kishiya

“Hauwa ta sossoka wa ‘ya’yanta wuka wanda hakan ya kawo ajalinsu,” Sadiq Aminu yace.

Dagacin Diso, Malam Ahmad Bello, ya nuna razanarsa da aukuwar lamarin ga manema labarai a jihar Kano a ranar Asabar.

Ya ce hakan ta faru ne bayan mahaifin yaran baya nan ya tafi gidan amaryarsa a safiyar Asabar.

Bidiyo: Abubuwan al’ajabi da baku sani ba game da Shugaba Buhari

Bello ya kushe wannan lamarin, inda yace a maimakon ta kai lamarin kotu, sai ta yanke hukuncin kashe ‘ya’yanta da kanta.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna yace rundunar ‘yan sandan ta fara bincike.

Amma kuma an tabbatar da cewa, har yanzu ba a ga mahaifiyar ba domin ta tsere.

What's On Your Mind?