Tukfa Da Warwara Game Da Shigowar Boko Haram Bauchi

- Advertisement -

Tukfa Da Warwara Game Da Shigowar Boko Haram Bauchi

Daga Khalid Idris Doya,

A wani abu da za a iya fassara shi da tufka da warwara, an shiga rudani dangane da gaskiyar maganar cewa mayakan boko haram solar shiga wasu yankuna na Jihar Bauchi daga yankin Gaidam na Jihar Yobe.

Al’amarin mai matukar daure kai ya auku ne a ranar Litinin bayan wani taron manema labarai da sakataren gwamnatin jihar ya yi bayani a kan bullar wasu masu aikata miyagun laifuka a yankunan hudu wanda su kuma ‘yan jarida suka fassara da boko haram ne.

Gwamnatin ta Bauchi dai ta musanta rahoton da ke cewa ‘yan Boko Haram solar kai hari ko solar mamayi kananan hukumomin jihar guda hudu da suka hada da Gamawa, Zaki, Dambam da kuma Darazo.

Wakilinmu ya nakalto cewa a shekaran jiya zuwa jiya ne dai wasu daga cikin manya da jaridun kasar nan suka yada labarin da ke cewa akwai matsalar tsaro da ake fuskanta a Jihar Bauchi, inda jaridun suka dogara da cewa solar samu bayanin ne daga wani taron manema labarai da sakataren gwamnatin Jihar Bauchi, Muhammad Sabiu Baba ya yi jimkadan bayan taron majalisar tsaro ta jihar.

 

An dai bada rahoton cewa ‘yan ta’adda solar shigo Bauchi ta Gaidam wanda hakan ya jawo ma suka lalata ofishin kamfanin sadarwa na MTN a karamar hukumar Gamawa, kodayake al’ummomin yankin solar nuna makamakinsu kan labaran da cewa suna zaune lami-lafiya.

 

Fitar labaran ke da wuya ya janyo cece-kuce inda gwamnatin ta fito ta ce sam ita ba ta bayyana cewar Boko Haram solar shigo cikin jihar ba, kana rundunar ‘yan sandan jihar ma ta karyata rahoton.

 

A wani taron manema labarai da babban mai baiwa gwamnan jihar Bauchi, shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Kwamared Mukhar Gidado, ya bayyana cewar ‘yan jaridan solar yi riga-malam masallaci, domin kuwa babu inda aka bayyana musu cewar Boko Haram solar dira a Bauchi, bihasalami, sakataren gwamantin jihar bai ce ‘yan Boko Haram solar shigo Bauchi ba.

 

Ya yi bayanin daki-daki kamar haka: “Jiya (shekaran jiya) Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya kira taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta jihar Bauchi kuma dukkanin mambobin Majalisar solar halarci wannan taron tare da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomin da lamarin ya shafa. Bayan kammla taron Gwamna ya umarci Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi da ya yi wa ‘yan jarida bayanin zaman, indai Sakataren Gwamnatin ya yi jawabi wa ‘yan jarida da ke bayanin yanayin tsaro da kananan hukumomi hudu ke ciki da suka hada da Zaki, Gamawa, Dambam da Darazo.

 

“Ya shaida wa ‘yan jarida cewa sakamakon farmakin da ‘yan Boko Haram suka kai a garin Gaidam an samu ‘yan gudun hijira da suka gudu zuwa kananan hukumomin nan da suke Jihar Bauchi kuma suna zaune a cikin kananan hukumomin da kauyukansu.

 

“Haka zakila Sakataren Gwamnatin ya sanar da ‘yan jaridan cewa gwamnati ta bada wani kasida wa Kwamitin tsaro na jihar domin a bi kasidar don tabbatar da tsaro a wadannan kananan hukumomin hudun wanda ya tabbatar da cewa za a bi wannan matakin sau da kafa domin tabbatar da cewa ‘yan gudun hijira da suka shigo da farmakin ‘yan Boko Haram a Gaidam bai shafi zaman lafiyar jihar Bauchi ba.

 

“Sannan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakai domin ya tabbatar da hatsaniyar da ke jihar Yobe bai shigo cikin jihar Bauchi ba domin muna da iyaka da jihar Yobe. An umarci jami’an tsaron da su dauki matakan kare iyakokin Bauchi da jihar Yobe.”

 

“Har-ila-yau, SSG din ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro solar kama wasu bata gari biyar wadanda suka je turke na MTN suka ciccire kayayyaki nan da nan an kama su kuma ana cigaba da bincike a kansu.”

 

Ya kuma ce Gwamnatin ta dauki matakin tashi tsaye da sanya ido a kananan hukumomin domin shirin ko ta kwana don gudun kada matsalar tsaro ya barke a jihar.

 

“Bayan wadannan jawaban nasa, lokacin da ‘yan jarida suka tashi fitar da labaransu sai wasu daga cikin manyan jaridun kasar nan suka bada rahoton cewa kungiyar Boko Haram ta kai farmaki a kananan hukumomi hudu a Jihar Bauchi. To, gaskiya lamarin nan ya zo mana da mamaki, domin labarin ba haka ba ne ba daidai ba ne, ba kuma gaskiya ba ne, domin shi Sakataren Gwamnatin da Gwamnatin ba su fadi hakan ba.”

 

Kan hakan, Gidado ya bayyana cewar Gwamnatin jihar ya dauki matakan da suka hada da bayyana wa al’ummar jihar da su yi watsi da duk labarin da ke cewa Boko Haram solar shigo Bauchi, yana mai cewa babu wata karamar hukumar da ‘yan Boko haram suka shiga a jihar Bauchi.

 

“Wasu jaridu ne suka yada hakan, tunin ma daya daga cikin manyan jaridun da ita ma ta fitar da wannan labarin ta gyara kuma ta bada hakuri. Gwamnatin Bauchi ta lura da cewa Jaridar  ta ce ta yi wannan rahoton bisa kuskure ta kuma bada hakuri. Saboda haka muna kira ga sauran ‘yan jaridun da suka bada wannan rahoton muna bukatar su janye wannan labarin nasu su kuma gyara kamar yadda Jaridar ta yi.”

 

Daga bisani Gidado ya jawo hankalin ‘yan jarida da cewa lamarin tsaro ba abu ne da ya dace a yi wasa da shi ba, ya nemi da suke aikinsu bisa kwarewa da sanin ya kamata domin kada su tayar wa al’umma da hankali.

 

Bayan hakan Kakakin Gwamnan ya kuma bayyana cewar nan take gwamnan jihar Bauchi ya umarci a kai kayan tallafi wa ‘yan gudun hijiran da suka kwararo zuwa jihar domin taimaka wa rayuwarsu da kokarin fitar da su daga cikin kucin rayuwa da suka fada.

 

kananan hukumomi biyun da za a kai wa ‘yan gudun hijiran tallafin solar hada da Gamawa da Dambam da suka yi kaura zuwa Bauchi sakamakon harin da ‘yan Boko Haram suka kai musu a Gaidam, lamarin da ya tilasta musu arcewa daga muhallansu na asali.

 

Muktar Gidado ya bayyana adadin kayan abinci da za a raba wa ‘yan gudun jiran da cewa buhun shinkafa, 1,750, buhun masara 1,050, buhun dawa 1,750, katan-katan na taliyar sufageti 1,050, buhunan suga 350, katan na Indomie.

Ita ma rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta karyata rahotonnin shigowar ‘yan Boko Haram jihar, inda ta ce labaran babu gaskiya a ciki.

 

A sanarwar manema labarai da Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Waki, ya bayyana cewar labaran da kafafen yada labarai suka yada, solar jingina da cewa solar samu bayanin ne daga bakin sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Sabiu Baba wanda ya bayyana musu bayan wani taron zama na gaggawa kan tsaro da masu ruwa da saki suka yi karkashin jagorancin Gwamna Bal Muhammad a a gidan gwamnati ranar Litinin.

Wakil, ya ce zaman da masu ruwa da tsaki suka yi kan tsaro, an yi ne bisa rahotonnin shigowar wasu mazauna Gaidam da Kanamma da suke jihar Yobe bayan harin da ‘yan Hoko Haram suka kai yankunan.

“A zaman da aka yi, SSG ya bayyana cewar an tattauna domin ganin an dauki matakan da suka dace tare da samar da wadaccen tsaro domin kare jihar daga abubuwan da suke faruwa a jihohin makwabta.

 

Ya kuma bayyana cewar wadanda suka kama bisa zargin satar kayan sadarwa yanzu haka suna kan bincike a kansu.

 

A don haka ‘yan sandan suka ce babu wani dan Boko Haram da ya shigo Bauchi, “Muna kira ga jama’a da su yi watsi da labaran da ke cewa ‘yan Boko Haram solar shigo Jihar Bauchi, sannan su cigaba da tafiyar da harkokin rayuwarsu na yau da gobe.”

Daga nan dai ‘yan sandan solar nemi jama’a da suke kai musu rahoton dukkanin wani motsin da suka gani domin daukan matakan da suka dace.

 

- Advertisement -