Bidiyo: Tsohon ministan Najeriya yana dukan matarsa

0
141

A cikin kwanakin nan ne aka dinga rade-radin rabuwar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da matarsa mai suna Valuable Chikwendu.

Wannan lamarin ya janyo matukar cece-kuce daga jama’a da dama.

Bayan fitowar rade-radin, tsohon ministan ya fito ya musanta rabuwarsu inda yace har yanzu suna tare.

A ranar Asabar da ta gabata kwatsam sai ga bidiyonsa yana dukanta inda take nadar bidiyon da kanta.

Tsohon ministan Najeriya yana dukan matarsa

A wani labari na daban, tsohon ministan harkokin sufurin sama, Femi Fani Kayode (FFK), ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kan cewa yana shirin sake aure duk da har yanzu da sauran rigima tsakaninsa da tsohuwar matarsa da yanzu basa zaune tare.

Bidiyo: Yadda Namiji ke Tona manyan sirrin ‘yan Arewa

A ranar Litinin ne tgsohon ministan ya yada wani hotonsa tare da wata kyakyawar budurwa da aka gano cewa sunanta Halima Yusuf.

Ganin hotunan tare da zukekiyar budurwar solar haddasa cece-kuce da yada gulmar cewa FFK na shirin sake yin aure a karo na biyar.

FFK ya yada hotunan ne daidai lokacin da rikicinsa da matarsa ta hudu, Valuable Chikwendu, suke kara zafi, wata alama da ke nuna cewa aurensu ya lalace.

Sai dai, da ya ke mayar da martani a kan cecekucen da jama’a ke yi, FFK ya karyata jita-jitar cewa aure zai kara tare da bayyana cewa Halima ”kawatace da ke da kusanci da ni, na yarda da ita.”

What's On Your Mind?