Tsohon Gwamna Legas, Tinubu babu lafiya, an fitar da shi zuwa wani asibitin waje

0
151

Jaridar The Cable ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kwanta jinya a garin Faris, kasar Faransa.

The Cable ta fahimci cewa fitaccan ‘dan siyasar bai da lafiya, kuma abin ya kai an kwantar da shi a wani babban asibiti da ke kasar ta Turai.

Tsohon Gwamna Legas, Tinubu babu lafiya, an fitar da shi zuwa wani asibitin waje

Sai dai akasin jita-jitar da ke yawo, Bola Ahmed Tinubu bai kamu da kwayar cutar COVID-19 ba.

Rahotanni solar tabbatar da cewa an yi wa Bola Tinubu gwajin Coronavirus kafin ya tafi Ingila a Disamba, kuma an tabbatar cewa bai da cutar.

An dauki tsawon sa’o’i 3 a jeji, jirgin kasan Najeriya ya tsaya a hanya

Babban jigon na jam’iyyar APC mai mulki ya bar Najeriya zuwa Ingila a watan da ya wuce ne bayan ya koka da cewa gajiya na damunsa.

A karshen makon nan ne aka wuce da ‘dan siyasar zuwa wani asibiti da ke birnin Faris, Faransa.

Mai magana da yawun bakin ‘dan siyasar, Tunde Rahman, ya musanya rade-radin cewa Coronavirus ko wata cuta ta fitar da Tinubu.

Rahman ya ce: “Labarin ba gaskiya ba ne. Asiwaju ya na da lafiya, bai dauke da kwayar cutar COVID-19. Ya yi tafiyarsa ta karshen shekara ne”

Tsohon Gwamna Legas, Tinubu babu lafiya, an fitar da shi zuwa wani asibitin waje

Hadimin ya tabbatar da cewa: “Wajen shirin tafiyar, ya yi gwajin COVID-19, aka tabbatar bai kamu ba Tun da aka fara cutar, ya na kaffa-kaffa.”

Mai magana da yawun Tinubu ya hakikance a kan cewa ya bar Najeriya ne domin ya huta kamar yadda ya saba duk shekara, ba jinya ta kai shi ba.

A kwanakin bayan nan ne aka ji Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ta’aziyyar rashin mahafinsa.

Bola Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan Hakimin Madobi, ya ba shi gidan Aljanna Firdausi tare da fatan Allah ya ba iyalinsa hakurin jure rashinsa.

Jagoran jam’iyyar APC na kasan ya fitar da wannan jawabi ne a wata takarda da ya aikawa Kwankwaso.

What's On Your Mind?