Tsohon Alkalin Alkalai Na Jigawa, Ya Rasu A Hadarin Mota  

- Advertisement -

Tsohon Alkalin Alkalai Na Jigawa, Ya Rasu A Hadarin Mota   

Daga Munkaila Abdullah,

Wani mummunan hadarin mota yayi sanadiyyar rasuwar tsohon alkalin Alkalai na jihar Jigawa Alhaji Aminu Sabo Ringim.

 

Rahotanni solar tabbatarda cewa, hadarin ya faru a jiya Talata da misalin karfe 1:00 na rana a kauyen Shafar kan hanyarsa daga Dutse zuwa Ringim.

 

Kakakin rundunar tsoro ta farin kayan NSCDC SC Adamu Shehu ya tabbatarwa da majiyarmu  afkuwar al’amarin.

 

SC Shehu Yace,  hadarin ya faru yayin da marigayin ke tareda a cikin wata mota kirar fijo 206 wadda ta kwace a yayin da yake tuki.

 

Yace hadarin wadda ya ritsa da mutane biyu an garzaya dasu zuwa babban asibiti dake Ringim wadda daga bisani aka tabbatar da rasuwar yasa Shi kuma yaron nasa ya sami munanan raunuka.

 

Dan fatan Allah ya gafarta masa ya kuma baiwa iyalinsa da Al’ummar jihar Jigawa hakurin jure wannan babban rashi.

- Advertisement -