Tsawala Farashin Kayan Gine-gine Baisa “Yan Kasuwa Arziki – Tanimu Mada, Gusau

0
122

Tsawala Farashin Kayan Gine-gine Baisa “Yan Kasuwa Arziki – Tanimu Mada, Gusau

Babban dan kasuwa Sana’ar kayan gine-gine a Gusau, Alhaji Tanimu Mada, Gusau ya gargadi abokan sana’ar su ta kayan gine-gine da su daina tsawala farashin kayan su, ga masu saya don tsawala farashin baisa mutun yayi arziki.

Majalisar Dokokin Bauchi Ta Gargadi ’Yan Kwangila Bisa Aikata Ha’inci

Alhaji Tanimu Mada ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsa tanbayoyin dalibai masu sanin makamar aikin jarida a shagonsa da ke Gusau.

Kuma ya kara da cewa, Idan dan kasuwa ya sauka farashin kayan sana’arsa Allah zai sanya wa ribar da ya samu albarka kuma zai samu karin masu sayan kaya koda yaushe.
Kuma ya yi kira ga su ‘yan kasuwa da su rinka saida kayayyakin masu inganci, wanda kwararun kamfanoni ke kerawa inganta sana’ar su ta kasuwaci.

Da ya koma kan batun Gwamnati kuwa Tanimu Mada, ya yi kira gareta da ta hada gwiwa da manyan kamfanoni da masana’anta wajan tseda farashin kayayyakin dan saukaka wa talaka don samun damar gina mahalin cikin sauki.

What's On Your Mind?