Tsaro: Ko Taron Shan Shayi Gwamnonin Arewa Ke Yi Dama? (II)

- Advertisement -

Tsaro: Ko Taron Shan Shayi Gwamnonin Arewa Ke Yi Dama? (II)

A nan Arewaci gwamnoni solar sha yin taro don shawo kan matsalar Arewa, amma a fakaice wasu su na ganin taro ne kawai na yaudara, tunda tun-tuni solar saba yi wa jamaa gafara-sa, amma har yanzu ba su ga kaho ba.

Matakan magance matsalolin Arewa ba su bukatar yawan taron gwamnonin da su ka zame tarin tsintsiya ba shara, domin gwamnonin su na da halin bin tafarkin da zai tserar da jamaar su daga matsalolin da ke addabar su nan take, domin su ne ke da wuka, su ne kuma ke da nama a hannuwan su. Idan har ba su yi amfani da dukiyar talakawan da aka damka masu amana ba wajen cire masu kangin talauci da fatara, da kuma tashi tsaye wajen hada kai da gwamnatin tarayya don magance matsalolin da su ka zame wa yankin kakani-ka-yi tsawon shekaru ba, to ina amfaninsu a gare su? Talakawa su na kallon gwamnonin jihohi su ne babbar matsalar Nijeriya tunda solar kasa cire masu kitse a wuta.

An sha jin cewa za a magance illolin barace-barace, da rashin aikin yin da ya zame ruwan dare a jihohin Arewa, amma duk a banza, maimakon gwamnatin ma ta zage damtse wajen nemo dabarun magance hakan, sai kuma ta nemi yin kida bashi kuma za ta bata rawar ta da tsalle, wajen dulmiya mabaratan mummunar hanyar da ta fi barace-baracen illa.

Domin har yau din nan jamaan jihohin Arewar ce dai ke yawon bara a fadin tarayyar Nijeriya, ana ta kyarar su duk inda su ka kukkurda. Masanaantun Arewa kaf solar durkushe, an kuma yi watsi da aikin gona, jamaa na ta shiga bariki aikin ci-rani, wasu na faskaren itace, wasu na ga-ruwa, wasu na yankan farce, wasu na sayar da fetur ko bakin mai, wasu na yin dako da tura baro, wasu na sayar da jaridu, wasu kuma na gararamba a tituna, ba aiki sai ragaita ko zauna-gari-banza.

Jahilci da cututtuka solar fi yin katutu a Arewacin kasan nan, alhali kuwa dukiyar jihohin Arewa na da tarin yawa, kuma ba mai amfana daga gare ta sai shugabanni da yan barandar su. Wai shin ma su wadan nan gwamnonin da su ke fafitikar farfado da martabar Arewar da su ka ce magabatansu solar banzartar, za su kwatanta halaye irin na mazan jiya? Shin a yanzu haka su na nufin ba su san cewa hatta magunguna a asibitoci ko kayayyakin fida babu ba sai dai talakawa su yi ta bara a gidajen rediyo da talbijin kafin su samu dan abin da za a yi masu magani a asibitocin da su ke cewa gwamnatocin da magabatan su su ka karbi milyoyin Nairori don kulawa da lafiyar jamaar su a banza? Baicin haka nan wace dabarar hadin gwiwa za su iya yi don tayar da masanaantun da su ka duddurkushe da sirafansu cikin kiftawa da bisimilla?

Kodayake dama wasu na yi wa gwamnatin kallon cewa duk kanwar ja ce, ja ya fado ja ya dauka ne, ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu, duk halayyar su guda, dabi’un su iri daya, ba su da bambanci sai bambancin jam’iyya, amma da waccan gwamnati da aka hambarar da kuma wannan kamar Danjuma ne da Danjummai.

An dade dai ana shan yan Arewa, kuma har yanzu ba su warke ba, amma sai dai solar kudurta aniyar cewa ba za su sake yarda gwamnoni da shugannin su su ci gaba da rarraba kawunan su, ko a yaudare su ba, domin an yi dogon dare, gari kuma ya waye. Gwamnonin Arewa su na da rawar takawa don magance matsalolin da su ka yi wa yankin dabaibayi amma solar buge da dogon barci.

Ka da a manta, ku san shika-shikan zabar wannan gwamnati shi ne don ta magance wa talakawan kasar nan matsalar tsaron da ta samo asali daga kungiyar Boko Haram, wadda ta kafa sansani a Arewa maso gabashin kasar nan, kuma su ke kai hare-hare a kasuwanni da wuraren ibadu.

Abinda ya tilasta wa jama’a neman canji kusan ko ta halin kaka, su na ganin watakila a samu sauki. Sai ga shi bayan nasarar gwamnatin APC sai harkar tsaron ta dauki sabon salo ta fuskoki da bangarori mabanbanta; kama daga garkuwa da mutane, kisan gilla da satar dukiyoyin jama’a da ‘yan fashin daji ke yi.

‘Yan bindiga solar raba daruruwan mutane da muhallin su, solar mayar da dubban yara marayu, inda matan aure su ka koma zawarawan karfi da yaji. Noma ya gagara a wuraren da matsalar tsaro ta yi kamari, yanzu ta abinda za a noma a ci ake yi ba wanda za a kai kasuwa domin biyan bukatar kai ba.

Da karshe ya kamata gwamnatin tarayya da na jihohi wadanda su na gagarumar rawar da za su taka wajen magance matsalar tsaron nan, da su kara zage damtse da bada kaimi wajen share hawayen talakawan da su ka zazzaga musu kuri’u har su ka kai ga matsayin da su ke kai yanzu.

- Advertisement -