Tsaro: Ba Za Mu Dagawa ‘Yan Bindiga Kafa Ba, Inji El-Rufai

0
154

Tsaro: Ba Za Mu Dagawa ‘Yan Bindiga Kafa Ba, Inji El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna ta tura wakilai zuwa iyalana daliban Greenfield da aka kashe domin yi musu ta’aziyya kamar yadda Wakilinmu ya ruwaito. A jawabinsa na ta’aziyya, kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna, Shehu Muhammed, yace gwamnati na nan akan bakarta na babu tattaunawar sulhu tsakaninta da ‘yan bindiga. Kwanakin baya dai wasu ‘yan bindiga suka kai hari jami’ar Greenfield dake jihar Ƙaduna inda suka yi awon gaba da wasu dalibai.

Tawagar wacce kwamishinan ilimi na jihar, Shehu Muhammed, ya jagoranta solar ziyarci iyalan mamatan a Jaji da Barnawa, Sabon Tasha dake Igabi da kuma karamar hukumar Chikun.

A jawabinsa, kwamishinan ya mika ta’aziyya ga iyayen daliban, sannan ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta fara kokarin kara matakan tsaro a kewayen makarantar. Ya kuma kara da cewa gwamnatin ta fara duba yiwuwar kwashe dalibai daga makarantun dake wajen gari zuwa wurin da take ganin yafi tsaro.

Kwamishinan ya jaddada matsayar gwamnatin na ba zata yi tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga ba, duk kuwa da matsanancin rashin tsaron da ake ciki a jihar.

What's On Your Mind?