… Tilastamu Aka Yi muka Katse Wutar Lantarki –Kamfanin Raba Lantarki

- Advertisement -

… Tilastamu Aka Yi muka Katse Wutar Lantarki –Kamfanin Raba Lantarki

Daga Yusuf Shu’aibu,

Kamfani samar da wutar lantarki a Nijeriya (TCN) ya bayyana cewa, tilasta masa aka yi har ya katse wutar lantarki a Jihar Kaduna, sakamakon matsin lamba da ya samu daga wajen kungiyar kwadago.

Kungiyar gwadugo (NLC) ta shelanta gudunar da yajin aiki na gargade har na kwanaki biyar, wanda ya fara aiki tun daga ranar 16 ga watan Mayu ta shekarar 2021, a Jihar Kaduna, sakamakon korar ma’aikata masu yawa da gwamnatin jihar ta yi a kwanakin baya. An dai katse wutar lantarki a daukacin jihar ne a ranar Lahadi, wanda ya sa al’ummar jihar suka fara zama a cikin duhu.

Kamfanin rarraba wutar lantarki a Jihar Kaduna (DisCo), wanda ke bai wa jihohin Kaduna, Kebbi, Sakkwato da kuma Zamfara ya sanar da cewa, zai katse aikinsa sakamakon matakin da kungiyar gwadugo ta daukan na shiga yajin aiki.

A cikin bayanin jami’in yada labara na wutar lantarki a Jihar Kaduna, Abdulazeez Abdullahi ya bayyana cewa, “mahukunta na samar da wutar lantarki suna bakin cikin sanar da daukacin mutanen Jihar Kaduna masu amfani da wutar lantarki cewa, ayyukansu zai katse a cikin jihar sakamakon matakin da kungiyar gwadugo ta daukan na shiga yajin aiki.

“Bisa umurnin da kungiyar gwadugo ta bai wa kamfanin samar da wutar lantarki a Nijeriya, ya katse gaba daya wayarsar mai lamba 33KB wacce ta bai wa Jihar Kaduna wutar lantarki.

“Bayan haka, muna rokon dukkan al’umma da jami’an tsaro da kungiyar sa-kai da su saka ido wajen kulawa da kayayyakin wutar lantarki, domin kar a lalatasu ko kuma a sace. Su yi kokarin kai rahoton duk wani zirga-zargan da su amince da shi ba a kusa da tirasfoma zuwa wajen hukuma.”

Jaridar MOBILIZED9JA ta ruwaito cewa, yajin aikin da kungiyar gwadugo ta kira a jihar ya samu karbuwa, domin  kuwa kungiyar masu dakwan man fetur da gasoline solar umurci ma’aikatasu da su dakatar da ayyukansu a Jihar Kaduna tun daga ranar 16 ga watan Mayu. Sakataren kungiyar masu dakwan man getur da gasoline, Mista Afolabi Olawale shi ya bai wa direbobin wannan umurnin a ranar Laraba. Olawale ya bayyana cewa, wannan umurnin yana da matukar mahimmanci, domin samun nasarar a kan yajin aikin da ake yi a jihar, bisa yadda gwamnan Jihar Kaduna yake azabtar da ma’aikatan jihar.

Kungiyar masu dakwan man fetur da gasoline ta bayyana cewa, ta bi umurnin da kungiyar gwadugo ta bai wa ma’aikata jihar na gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar wanda ya fara tun daga ranar 16 ga watan Mayun shekarar 2021.

An dai bayar da wannan umurnin ne sakamakon korar ma’aikata sama da four,000 da gwamnatin jihar ta yi a kwanakin bayar.

Shugaban kungiyar gwadugo na Jihar Kaduna, Mista Ayuba Suleiman ya bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne bayan kammala taron gaggawa da wakilan kungiyar gwadugo na kasa, wanda ya gudana a Jihar Kaduna. Kungiyar gwadugo tana zargin gwamnatin jihar da saba ka’ida wajen korar ma’aikata guda four,000 daga kananan hukumomin da hukumar ilimi ta jihar da ma’aikatar lafiya na matakin farko.

A cikin sanarwar da kamfanin TCN ta fitar wanda yake dauke da sahannun shugaban kamfanin da jami’i yada labarai, Ndidi Mbah solar tabbatar da daukan wannan mataki, inda suka bayyana cewa an katse wutar lantarki ne a Jihar Kaduna sakamakon matakin yajin aikin da kungiyar gwadugo ta shiga.

Sanarwar ta bayyana cewa, “kamfanin TCN ya samu matsin lamba daga kungiyar kwadago a jiya wanda ya tursasa shi katse dukkan wayar wutar lantarki mai lamba 33KB da ke bai wa Jihar Kaduna wutar lantarki. Wannan ne ya sa dole muka dauki matakin tsayar da ayyukanmu a Jihar Kaduna, sakamakon yadda kungiyar gwadugo ta matsa mana, wanda a yanzu gaba daya jihar babu wajen da za a samu wutar lan

- Advertisement -