Tasirin Yajin Aiki: Kaduna Ta Dau Dimi

- Advertisement -

Tasirin Yajin Aiki: Kaduna Ta Dau Dimi

Daga Shehu Yahaya,

Cikin garin Kaduna ya dau dimi a ranar Litinin yayin da ma’aikatan sassan gudanar da harkokin rayuwa suka ba da hadin kai ga kungiyoyin kwadago wajen tsunduma a yajin aikin gargadi na kwana uku da aka fara, da nufin matsin lamba ga gwamnatin jihar ta sauya shawara kan dubban ma’aikatan da ta kora.

Har zuwa lokacin da muke kammala rubuta rahoton nan al’amura a babban birnin jihar, Kaduna solar yi tsaye cik, saboda bankuna ba sa aiki, babu wutar lantarki da ruwan sha da dai sauran bangarorin extra rayuwa.

Hakazalika, kungiyoyin kwadagon a karkashin NLC solar garkame duk wata ma’aikatar gwamnati da ta yi biris da shiga yajin aikin.

 

Kungiyar kwadagon ta NLC reshen Jihar Kaduna ta bayyana cewa yajin aikin da ta fara babu gudu babu ja da baya, matukar gwamnatin jihar ta gaza cika muradun ma’aikatan jihar.

 

Kungiyar ta ce tun farko gwamsnatin jihar ta yaudare su kan cewa za ta biya mafi karanci albashi na Naira dubu 30 amma sai daga baya gwamnatin ta ce ba za ta iya biyan ba da sauran hakkokin ma’aikata.

 

Bayanin hakan ya fito ne daga shugaban kungiyar kwadagon, reshen Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, a jawabin da ya gabatar yayin fara zanga-zagar yajin aikin na kwana biyar da aka fara jiya.

 

Ayuba Magaji Suleiman ya ce “Tun farko gwamnatin ta yaudare mu a kan cewa ita ce za ta fara biyan albashi mafi karanci na Dubu 30 ga ma’aikata da wadanda suka bar aiki sai daga baya muka gano cewa gwamnatin ba za ta iya biya ba”

 

” A watan jiya wato watan Afrilu sai muka ga gwamnatin tana biya ma’aikata a tsarin Naira dubu 18 mafi karanci  albashi wanda kuma a hakan sama da ma’aikata dubu 20 rabin albashi aka basu wanda bai kai Naira dubu 18 ba, wannan mataki da gwamnatin Jihar Kaduna take dauka ba mu amince da shi ba”

 

“Haka a bangaren ma’aikata na lafiya duk hakkokinsu gwamnati ta gaza biya musu wanda kuma wajibi a biya su, alal misali, idan za a tura ma’aikacin lafiya kauye babu wata gudummawa da gwamnatin take basu wai kuma a haka ake so su yi aiki” in ji shi.

 

Ayuba Suleiman, ya nuna damuwarsa a kan ikirarin gwamnatin na cewa ta biya Naira Biliyan 14 na kudin Ariyas ga ma’aikata dubu 35 da ta kora a shekarar 2017 amma har yanzu kashi 80 cikin 100 ba su sami ko Naira ba wanda yanzu da yawansu rayuwarsu tana cikin mawuyacin hali.

 

Shugaban ya kara da cewa ma’aikatan Jihar Kaduna su ne kadai ma’aikata da ba sa zuwa karo ilimi a fadin kasar nan baki daya amma kullum sai (gwamnatin) ta pretend da cewa ba su cancanta ba.

 

Kungiyar ta ce daga hawan Gwamna el-Rufa’i zuwa Litinin din nan ya kori dubban ma’aikata ba tare da biyansu hakkokinsu ba, suna masu cewa dadin bakin da gwamnan ya yi ta musu shi ne ya hana su shiga yajin aiki tuntuni.

- Advertisement -