“Tashin Hankalin Da Muka Gani A Gaidam”

0
231

“Tashin Hankalin Da Muka Gani A Gaidam”

Daga Hafsat Moh’d Arabi

Misalin karfe 11 Na Secure Suka Fara Yanka Mutane
Wasu Ruwa Kawai Suka Sha Suka Zarce Da Azumi
Tun karfe Biyar Na Yamma Suka Fara Harbe-harbe Har Gari Ya Waye

 

Wata uwa tare da iyalinta da ta samu tsira daga harin da mayakan boko haram suka kai garin Gaidam a Jihar Yobe kwanan nan, ta bayyana irin tashin hankalin da suka gani a garin, yayin da mayakan suka kai farmaki a ranar Juma’a da dare.
Matar wacce muka yi mata suna da Falmata saboda ta nemi a boye sunanta, ta bayyana cewa solar tsinci kansu a wani mawuyacin hali tare da ganin mutuwa kuru-kuru da idanunsu.
Ta fara da shinfida kan yadda lamarin ya auku kamar haka: “Tun ranar Juma’a kungiyar boko haram suka shigo garin, karamar Hukumar Gaidam ta Jihar Yobe, misalin karfe biyar na yamma. Tun shigowarsu muka fara jin karar bindigogi da bomb.”
Ganin cewa ana cikin watan Azumin Ramadan ko yaya abin ya riske su ganin cewa an kusa shan ruwa lokacin da aka kawo harin?
“Akwai wadanda suka samu suka fita a kafa a garin kafin lokacin shan ruwa, lokacin shan ruwa ya yi ba su samu abin bude baki ba ruwa kawai suka sha har washe gari suka zarce da sabon azumi. Mu kuma muna cikin garinmu ba mu samu mun fita ba a lokacin, tun karfe biyar na yamma da suka shigo suka fara harbe-harbe ba su daina ba har gari ya waye.” In ji ta.
Ta fuskar sadarwa kuwa, Falmata ta ce mayakan solar yi mummunar ta’adi, domin kuwa “solar kona hanyoyin sadarwa na garin gaba daya, yanzu haka babu community a garin, solar shiga shaguna solar kwashe kayayyakin abinci solar fita da shi cikin daren juma’a,
Kafin gari yawaye wasu motocin su na kungiyar Boko Haram suka sake shigowa garin su tara.”
To ko a wane hali suka ga zuwan sojojin Nijeriya da suka kawo musu dauki, Falmata ta nunar da cewa abin ba dadi, “Da gari yawaye da safiyar Asabar aka turo jirgin air Drive ya fara harbi, ta sanadiyar haka mutane 11 suka rasa ransu a gida daya lokaci daya jirgin ta jefa musu bomb suka kone, ta dalilin haka ko jana’iza ba su samu ba a cikin garin, sai da aka fitar da su wani kauye kusa da Gaidam aka yi musu jana’iza.”
Abin ba tsaya nan, bayan gari ya waye ne sai boko haram din suka fara yi wa mutane kisan gilla a zahiri. Ga ci gaban bayanin Falmata, “Misalin karfe 11: na safiya (boko haram) suka fara yanke wa mutane kai, sojoji solar gudu solar bar garin, jirgin da aka turo na Air Drive shi ma ya koma. Tun da suka fara yanke wa mutane kai, kowa ya fara neman hanyar fita ya bar garin ko ta halin yaya ne.
“Babu damar a daidaita sahu su fita ko motoci, sai dai ka fita da kafafuwanka shi ma ta bayan gari hanyar da boko haram din ba su bi ba. Mu ma mun samu mun fito da kafafuwanmu mun je wani kauye mun yi tafiyar kilomita da dama a kafa, akwai wadanda suka rasu a hanya saboda solar jikkata ga kishirwa ga yunwa, an musu jana’iza a kan hanya.”
To ko a wane hali iyalai suka kasance cikin irin wannan masifa, Falmata ta yi karin bayanin cewar, “ Wasu tun ranar Juma’a suka bar ‘ya’yansu da matansu kuma har yanzu ba su hadu ba, akwai matar da ba ta san inda mijinta yake ba shi ma bai san inda take ba gashi babu Sabis.
“Wadanda aka yanke musu wuya tun Asabar har yanzu gawar tana inda take babu wanda ya je kusa da ita saboda tsoron abin da zai similar su.
“A takaice dai yanzu babu sauran mutane a cikin garin Gaidam sai boko haram ne suka mamaye garin su kadai, yau (ranar Litinin) kwanansu hudu a ciki…solar yi kone-kone da kashe-kashen al’umma.” In ji Falmata.
Rundunar Sojin Nijeriya dai tana ci gaba da kokarin tabbatar da kwanciyar hankali ya dawo a garin na Gaidam.

What's On Your Mind?