Tashin Hankali A Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Dalibai Uku Cikin Wadanda Suka Sace

0
135

Tashin Hankali A Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Dalibai Uku Cikin Wadanda Suka Sace

Bayanan da muke samu daga Gwamnatin Jihar Kaduna na cewa ‘yan bindigar da suka sace daliban jami’a Greenfield mai zaman kanta da ke hanyar Kaduna-Abuja solar halaka guda uku daga cikinsu.

Kamar yadda wata sanarwar da ke dauke da sa hannun Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar, Malam Samuel Aruwan ya Sanya wa hannu aka raba wa manema labarai ta tabbatar da cewa an tsinci Gawar daliban guda uku a mace.

A wani tsarin da ke nuni a fili cewa akwai matsalar rashin hankali tattare da rashin tausayi a irin yadda ‘yan bindigar suka kashe daliban da suka sace a cikin jami’ar Greenfield tsawon milimita 34 Kan titin Kaduna zuwa Abuja.

In dai ba a manta ba, ranar Talata ne da ta gabata da dare wadansu ‘yan bindigar da ba a gane yawan su zuwa yanzu ba suka kutsa kai cikin jami’ar da ke Kauyen Kasarami cikin karamar Hukumar Chikun suka yi awon gaba da daliban.

An dai tsinci Gawar daliban ne a yau Juma’a a kauyen Kwanar Bature, wani kauye ne kusa da jami’ar, kuma Kwamishinan harkokin cikin gida na Jihar Kaduna da kwamandan Thunder strike, Laftanar Kanar MH Abdullahi solar kwashe gawarwakin zuwa wurin ajiye gawa na asibiti.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmad El- Rufa’I tuni ya yi Allah wadai da wannan kisan da ya bayyana da rashin hankali, inda ya ce hakika wadannan yan bindiga solar bayyana tsananin rashin Imani ga rayuwar dan Adam don haka dole ne a yake su kamar yadda suka bukaci yin hakan.

Gwamnatin ta yi bayanin cewa za ta ci gaba da bayar da bayanin abin da yake faruwa recreation da lamarin.

Wannan rashin imani na wadannan mutane yana zuwa a daidai lokacin da jama’a ke ta kiraye-kirayen cewa ya kamata Ggwamnan jihar Kaduna ya sauko daga matsayinsa na bijire wa tattauamawa da wadannan miyagu.
Inda wasu jama’a ke nuni da cewa ko da ba za a bjya diyyar da suja nema ba, amma yana da kyau a tattauna da su a ji matsalokin su.

What's On Your Mind?