HOTUNA: Taron Kaddamar Da Gina Jami’a da gagarumin wa’azin kasa A Hadejia

0
288

Shugaban kungiyar JIBWIS Ash-Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, tare da shugaban majalisar malamai Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, da daraktan agaji Engr. Mustapha Imam Sitti, na gayyatar al’ummar musulmi zuwa kaddamar da aza gina jami’ar ‘As-salam Global University’ a garin Hadejia jihar Jigawa a Naijeriya.

Sheikh Bala Lau yace za’a gabatar da meeting na majalisar EXCO ta kasa a ranar juma’a 9-10-2020.

Sannan washe gari asabar 10-10-2020 za’a gabatar da meeting da Dukkan masu mukami a matakin kasa, da shugabannin kungiya na jihohi wadanda suka hada da; Shugaban kungiya da sakatarensa shugaban malamai da sakataren sa, daraktan agaji da sakatarensa, daraktan Social Media da sakatarensa, daraktan ilimi da sakatarensa.

Taron Kaddamar Da Gina Jami’a da gagarumin wa’azin kasa A Hadejia

Kazalika za’a gabatar da gagarumin wa’azin kasa a ranar asabar da dare, Wanda dukkan Malamai da alarammomi na kungiyar zasu halarta insha Allah.

A ranar lahadi 11-10-2020. Kungiyar zata kafa babban tarihi wanda ake so ‘ya’yan kungiyar su jira ayi da su inda za’a wuce filin gina jami’a da dukkun ‘ya’yan ta inda za’a aza harsashin gina jami’ar ‘As-salam Global University’ (AGU) Mallakar kungiyar IZALA a garin na Hadejia cikin amincewar Allah.

Lewandowski Ya Lashe Kyautar Gwarzon Shekarar 2020 Na UEFA

Sheikh Bala Lau ya umurci mahalarta taro na na majalisar EXCO da su isa Hadejia ranar juma’a da wuri. Sannan sauran masu mukamai a matakin kasa, da shugabannin kungiya na jihohi wadanda aka gayyata da su isa Hadejia da wuri ranar asabar. Haka zalika sauran ‘ya’yan kungiyar da mahalarta wa’azin kasa wanda za’a gabatar ranar asabar da dare, suma su isa Hadejia akan lokaci.

Wannan taro ba’a daukewa kowa ba, matukar akwai lafiya da wadata.

Taron Kaddamar Da Gina Jami’a da gagarumin wa’azin kasa A Hadejia

Taron Kaddamar Da Gina Jami’a da gagarumin wa’azin kasa A Hadejia

Hakazalika Har yanzu kofar neman taimako na gina jami’a a bude take, muna kira ga kowa da kowa ya bada sadakar sa da iyalansa da iyayensa, mai gudana a kalla ₦1000 ga ko wanne, ko sama da haka domin gina wannan makaranta, muna muku albishir da lada zaiyi ta samunku ko da bakwa raye inji Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi.

Acc Name: As-salam Int’l University
Acc No: 0006027065
Bank: Ja’iz

Allah ya bada ikon zuwa da taimakawa. Amin.

Sanarwa daga Sakataren kungiyar ta kasa, Sheikh Dr. Muhamnad Kabir Haruna Gombe, kai tsaye ta ofishin darakta Jibwis Social Media ta kasa.

#Jibwis_Nigeria

 

What's On Your Mind?