Tarihin Yadda Mai Trailer 17 Da Dukiya Da Dama Ya Zama Mahaukaci

- Advertisement -


Wannan bawan Allah da kuke gani haka a da kafin ya koma haka mutum ne mai ilimin addini da na boko kuma yana da arziki mai tarin yawa sosai matansa biyu yaransa biyar, yana da manyan motoci tilera guda 17 amma yanzu ba shi da komai.
Sakamakon Allah Ya yi mashi Nafsi na ɗaukaka a wajen kasuwancin sa shine wasu ke zargin cewa abokan kasuwancin sa suka sa shi a gaba ƙarshe dai har sai da suka cika burinsu akan shi inda su kai sanadiyar mai da shi ya zama mahaukaci.

Duk tarin ƴaƴa da ƴan’uwan sa sun yi iyakar bakin ƙoƙarin su akan shi har sun gaji.

Yanzun ƴan’uwan sa sun ce suna bukatar barar addu’a daga gare ku Allah Ya ba shi lafiya.

- Advertisement -