Tantance Na Bogi: Gwamnatin Gombe Ta Dakatar Da Ma’aikata 668

0
61

Tantance Na Bogi: Gwamnatin Gombe Ta Dakatar Da Ma’aikata 668

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnatin Jihar Gombe ta ce ma’aikata 668 ne ta dakatar da tura musu kudin albashi na wata-wata da suka kunshi ma’aikatan hukumomin jihar 431, karamar hukumar Akko 134 da kuma na karamar hukumar 103.

Idan za ku iya tunawa dai a baya-bayan nan gwamnatin jihar ta kawo wani na’urar da zai tantance ma’aikatan bogi da na zahiri a jihar domin dakile masu ci da gumin wasu.

Kwamishinan kudi na jihar, Muhammad Gambo Magaji, ya shine ya sanar da dakatar da akalla ma’aikata 668 a jihar, sakamanon fara aiwatar da shirin nan na tantance ma’aikata da na’urori masu kwakwalwa.

Ya ce wadanda lamarin ya shafa basu bayyana ba don tantancewar, don haka aka dakatar da albashin su daga jadawalin biyan ma’aikata na jihar.

Ya ce ma’aikata 431 da dakatarwar ta shafa solar fito ne daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati 84 dake jihar.

Ya kara da cewa an fara gwajin shirin ne a kananan hukumomin Gombe da Akko ciki har da sashin ilimi na kananan hukumomin biyu.

A cewarsa a karamar hukumar Gombe kimanin ma’aikata 103 ne basu bayyana don tantancewar ba, da suka hada da ma’aikatan karamar hukuma 44 dana sashin ilimi 59.

Kwamishinan ya bayyana cewar jihar ta samu ceto naira miliyan 38 daga ma’aikatan da ta dakatar sakamakon kin bayyana a gabanta domin tantancewar zahiri.

Ya kuma bayyana cewar dukkanin ma’aikatan jihar daga hukumomi da rassan jihar dukka za a tantance su, wanda hakan na daga cikin kokarinsu na gano ma’aikatan zahiri da kuma na bogi ne.

What's On Your Mind?