Tabbas Na Kai Wasu ‘Yan Kwangila Wurin Buhari Amma… – Rabaran Mbaka

0
97

Tabbas Na Kai Wasu ‘Yan Kwangila Wurin Buhari Amma… – Rabaran Mbaka

Daga Yusuf Shu’aibu,

Babban Paston cocin Adoration Ministry da ke Inugu, Reverend Father Ejike Mbaka ya amince da cewa ya kai wasu ‘yan kwangila su uku wajen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sai dai Mbaka ya yi ikirarin bai san da kwangilolin ba kafin a tattauna da shi, sai daga baya aka fada masu cewa zai taimaka ne wajen ceto Nijeriya daga rashin tsaro.

“Gaskiya ne na jagoranci masana tsaro zuwa fadar shugaban kasa, domin taimakawa wajen ceto Nijeriya daga yanayin rashin tsaro.

“Ban san su ba, amma dai solar zo waje na a Inugu suka roke ni a kan in hada su da gwamnati saboda yanayin rashin tsaro da yadda Nijeriya za ta kara ci gaba da fitar da mai a kasashen ketare. Mutane uku ne kuma na yi watsi da bukatarsu,” in ji Mbaka.

Mbaka ya bayyana haka ne lokacin da yake mayar da martani ga zargin da fadar shugaban kasa ta yi masa sa’ilin da ya bukaci shugaban kasa ya sauka ko a tsige shi, da cewa ya yi ne saboda an ki ba shi kwangila.

Paston ya goyi bayan Shugaba Buhari a lokacin zaben shekara 2015 da kuma 2019, a ranar Laraba da ta gabata ce lokacin da yake wa’azi, Paston ya bukaci shugaban kasa ya sauka saboda tabarbarewar tsaro a cikin kasar nan.

Mbaka ya bayyana rashin jin dadinsa a kan yadda Buhari ya yi shiru recreation da kashe-kashe da ake yi a cikin kasar nan, inda yake ganin ya gaza samar da tsaro.

“Abun mamaki ne bayan ya gama goyan bayan shugaban kasa a kan ya dare karagar mulki, a yanzu kuma Mbaka ya juya baya yana son shugaban kasa ya sauka ko a tsige shi.

“Mbaka ya juya bayar ne saboda an hana shi kwangila, shi ne ya nemi hucewa a kan shugaba Buhari,” in ji mashawarcin shugaban kasa, Garba Shehu.”

Mbaka ya bayyana cewa, bai jin tsoron fadar shugaban kasa, yana jin dadin yadda yake tsage gaskiya komin dacinta.

“Buhari ba zai iya ba domin yana fama da rashin lafiya da kuma tsufa.

“A wannan lokaci muna bukatar tsayayyen shugaban kasa. Idan suna tunanin saboda kwangila ne nake wannan maganar, to ba zan fasa magana ba ko za su gina babban jami’a a nan,” in ji Mbaka.

What's On Your Mind?