Tabarbarewar Tsaro: Majalisar Wakilai Ta Bukaci A Sanya Dokar Ta-baci

0
133

Tabarbarewar Tsaro: Majalisar Wakilai Ta Bukaci A Sanya Dokar Ta-baci

Majalisar wakilan tarayya ta yi zama inda aka yi muhawara a kan matsalar tsaro da ake fama da ita a kusan fadin kasar nan a halin yanzu.

A rahoton bayan zaman, majalisar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya dokar ta-baci a kan sha’anin tsaro. Majalisar wakilan ta na ganin cewa hakan ne kawai zai iya kawo karshen matsalar tsaro a fadin kasar nan.

Haka zalika a zaman da aka yi a yau, ‘yan majalisar solar yarda a gayyaci manyan shugabannin tsaro su bayyana a gabansu. Rahoton ya ce ‘yan majalisar su na son ganin mai ba shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Mongunu (mai ritaya). Har ila yau, ta bukaci duka hafsoshin sojoji na kasa da shugabannin hukumomin tsaro su bayyana a zauren majalisar domin su yi bayanin halin da kasa take ciki

Hafsoshin sojojin da ake sa ran za su hallara a zauren majalisa su ne; Janar Fortunate Irabor, Laftana-Janar I. Attahiru, Admiral A.Z Gambo, da Air Marshal I.O Amao

What's On Your Mind?