Sunday Igboho Ya Yi Barazanar Hargitsa Zaben 2023 A Yankin Kudu-Maso-Yamma 

- Advertisement -

Sunday Igboho Ya Yi Barazanar Hargitsa Zaben 2023 A Yankin Kudu-Maso-Yamma 

Daga Yusuf Shu’aibu,

Mista Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya gabatar da jawabi a Osogbo babban birnin jihar Osun lokacin da Yarbawa suke gudanar da zanga-zanga. A ranar Asabar ce, Sunday ya yi barazanar hargitsa zaben shekarar 2023 a dukkan jihohin Kudu-Maso-Yammacin Nijeriya. Ya yi ikirarin cewa, mafi yawancin gwamnonin Kudu-Maso-Yammaci suna bukatar ballawa daga Nijeriya, amma suna tsoron a daina ba su kudaden da ake ba su a duk wata idan suka goyi bayan samar da kasar Yarbawa.

“Ni ba matsoraci ba ne. Suna cewa za su kama ni. Wa zai iya yin hakan? A yanzu haka ba ma cikin Nijeriya. Ba mu da wani abun da ya hada mu da su a halin yanzu.

“Ba za a sake yin wani zabe ba a yankin Yarbawa ba har sai an bayar da kasar Yarbawa. Jami’an tsaron da suke kokarin tsorata ni a kan fafarukan da nake yi na neman kasar Yarbawa solar makara.

“Gwamnoninmu suna tare da ni. Tun daga jihohin Oyo da Ogun da Ondo har zuwa Ekiti da Legas da Osun, suna goyan bayanmu, amma ba za su iya fitowa su bayyana ba. Idan suka bayyana za a dakatar da ba su kudaden daga Abuja. Saboda haka ne suka yi gum da bakinsu. Na samar wa Gwamna Oyetola a garin Osun, shi ne ya amince da mu zo wannan wuri domin gudanar da zanga-zanga. Haka kuma dukkan sarakunanmu suna tare da mu,” in ji Sunday Igbohi.

Sai dai Mista Igboho bai bayar da wata shaida na wannan goyan yansa da gwamnonin suke yi. Ya bayyana cewa, zai saka kafar wando daya da dukkan masu ruwa da tsakim da suka kware masa baya.

Rahotanni solar bayyana cewa, Yarbawa masu neman kasarsu solar gudanar da zanga-zanga a babban titin garin Osogba, wanda suka kulle titin gaba daya. Suna ta kade-kaden kira a ba su kasarsu da kuma damun mutane da ke kan wannan hanyar. Kafin wannan zanga-zanga ta Jihar Osun, an taba samun irin wannan zanga-zanga a jihohin Oyo da Ogun a watan Afrilu da farkon watan Mayu.

Mafi yawa ‘yan Nijeriya solar bayyana cewa, sake sabon tsari ne kadai zai hana raba Nijeriya. Wannan ne ya sa gwamnonin 17 daga yankin Kudu-Maso-Yammacin Nijeriya solar bukaci a gudanar da taron sake sabon fasali a makon da ta gabata.

Fadar shugaban kasa ta bayyana bukatar sake sabon fasali zai iya kawo barazana ga hadin kai kasar nan, sai dai shugaban kasa zai aiwatar da wasu abubuwan na daban wanda zai hana raba kasar nan.

A baya dai, tarihi ya nuna cewa, shi Sunday Igboho kasurgumin shugaban ‘yan tawate ne. Wannan jaridar ta wallafa rahoton yadda aka kore shi daga garin Modakeke da ke cikin Jihar Osun a shekarar 2000, bayan samun rikici a tsakanin mambobin kungiyar masu motoci da ‘yan acaba. Daga baya dai Sunday ya fada dan barandar siyasar tsohon Gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja wanda a nan ne ya yi suna. A watan Junairu, ya jagoranci wata tawagar tun daga Igangan har zuwa Ibarapa na Jihar Oyo, domin kin amincewa da sarkin Fulani na garin Igangan, Salihu Abdulkadir wanda ya janyo hargitsi ga gwamnatin jiha da kuma ta tarayya. Ya zargin Mista Abdulkadir da goyan bayan mummunan ayyukan da Fulani ke gudanarwa na yin garkuwa da mutane da kisan manoma da ke wannan yankin. Sai dai Mista Abdulkadir ya musanta wannan zargin, amma dole ya tilasta masa barin garin na tsawan shekaru 10.

Haka kuma a cikin watan Fabrairu, ya karya dokar da gwamnatin Jihar Ogun ta saka na bai wa Fulani makiyaya wurin zama a Jihar. Ya yi ikirarin cewa, wasu jami’an tsaro daga Jihar Oyo solar yi kokarin kama shi a babban titin Jihar Legas zuwa Ibadab lokacin da yake tafiya zuwa taron manyan jihar wanda ya gudana a Ayo Adebanjo da ke Jihar Legas. Bai amince da jami’an tsaro na farinkaya da sauran jami’an tsaro na jihar ba. Ya taba yin barazanar farmaka manyan jami’an gwamnati da sarakunan Yarbawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Osun, Yemisi Opalola ba ta dauki kiran wayar da manema labarai suka yi mata ba, domin jin ta bakinta a kan wannan barazanar da Sunday Igboho ya yi a Osogbo a ranar Asabar.

- Advertisement -