SUBEB Ta Kafa Dokar Hukunta Malaman Makaranta Da Ke Makara A Neja

- Advertisement -

SUBEB Ta Kafa Dokar Hukunta Malaman Makaranta Da Ke Makara A Neja

Daga Muhammad Awwal Umar,

Hukumar kula da ilimin bai daya (SUBEB) ta bayyana cewar ta samar da doka dan hukunta malaman da ke zuwa aiki makare da ma wadanda ba su zuwa aiki a Neja. Mamba na uku na hukumar, Alhaji Abdukkadir Shehu Nahuntuwa, shi ne ya bayyana hakan ga manema labaru a Minna.

Nahuntuwa yace bayan zuwan gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello kan karagar mulkin jihar, solar fahimci cewar malaman makarantun faramare na fuskantar matsaloli da dama wanda ya kunshi rashin karin girma ga malamai da kuma matsalolin da malaman suka kirkirawa kan su na rashin zuwa aiki da ma wadanda ke zuwa aikin a makare, tilas hukumar ta fara daukar matakan gaggawa na tantance malaman makarantun faramare mallakin gwamnatin jiha da kuma samar da hukunci ga duk malamin da aka samu bai zuwa aiki da ma masu zuwa a makare, wanda zuwa yanzu dokar ta fara aiki a jihar.

Matsala ta biyu kuma lokacin mulkin gwamnatin jam’iyyar PDP da ta gabata, tsawon shekaru takwas malaman da suka cancanci karin girma ga a kara masu ba sai kusan karshen mulkin na ta, bayan karin girman kuma ba a dabbakar da shi ba ta yadda albashin su zai samu daidaito da karin da aka yi din.

Maigirma gwamna da yazo bayan karban rahoton duk da matsalolin kudi a lokacin ya umurci hukumar da ta tabbatar ta bi dukkan matakan da suka dace wajen ganin an daidaita albashin su ta yadda zai zo daidai da karin da aka yi masu din. Hukumar mu ba ta tsaya nan ba mun sanya shi ya zama dole duk shekara a dubi malaman da suka cancanci karin girna kuma zuwa yanzu an cigaba da mutunta malamai wajen bin doka da oda ta hanyar sauke masu nauyin da ya rataya akan gwamnati wajen ba su hakkinsu.

Abdulkadir ya cigaba da cewar akwai matsalolin lalacewar makarantu da kuma kirkirar makarantun da ba bu su a kasa alhalin ana cire kudaden gwamnati da sunan su, wasu na jefa kudaden a cikin aljihunsu. Yanzu SUBEB ta dakatar da wannan tare da mayar da hankali wajen gyaran makarantun da suka lalace, da zai baiwa yara karfin guiwar zuwa makaranta.

Daga cikin abubuwan da hukumar mu tayi shi ne daukar nauyin horar da malamai da shugabannin makarantun faramare sanin makaman aiki duba da yana daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati. Gwamnati jiha ta dauki bangaren ilimi da muhimmanci kan haka ne take baiwa hukumar bada ilimin bai daya karfin guiwar gudanar da ayyukan da suka dace da dawo da darajar ilimi a jihar. Dan saukakawa al’umma samun damar kai yara makarantu dan samun ilimin zamani a jihar.

Alhaji Abdulkadir Nahuntuwa ya shawarci iyayen yara da su taimakawa hukumar da shawarwari ta hanyar tuntubar hukumar SUBEB ko kuma sakatarorin ilimi na yankunan kananan hukumomi, hakan ba zai samu ba sai iyaye na bibiyar ‘yayansu akan abubuwan da ake karantar da su a makarantun su.

“Ya kamata a duk lokacin da yaro ya dawo makaranta iyaye su rika bincikar littafan yara a kullun suka dawo gida dan taimakawa hukumar sanin halin da makarantun ke ciki ta yadda za a iya gyara al’amurra. Hukumar mu a shirye take wajen daukar shawarwari da kuma daukar matakan da zasu ceto ilimin ‘yayan mu a jihar Neja”. Inji shi.

- Advertisement -