Luis Suarez Ya Zura kwallo Biyu A Wasansa Na Farko A Atletico Madrid

0
86

Dan wasa Luis Suarez ya ci kwallaye biyu ya kuma bayar da daya aka zura a raga a wasan farko da ya fara buga wa sabuwar kungiyarsa ta Atletico Madrid duk da saura minti 20 aka sa shi a karawar da kungiyar tasa ta buga.

Tun da fara buga wasan Atletico Madrid ta ci kwallo uku ta hannun Diego Costa da Angel Correa da kuma Joao Felid sai daga baya kuma Suares  wanda ya koma kungiyar daga Barcelona shima ya zura nasa kwallayen.

Suarez Ya Zura kwallo Biyu A Wasansa Na Farko A Atletico Madrid

Duk da cewa Suares daga baya ya shiga karawar, amma minti biyu da shiga fili, ya bai wa Marcos Llorente kwallo shi kuma bai yi wata-wata ba ya zura a raga kafin daga baya shima ya zura nasa.

Daga nan ne Atletico Madrid ta bugo kwallo ta hannun Llorente, sai dai nan da nan Suarez ya sa kai ta fada a raga sannan ya kara ta shiga kuma bayan an tashi babban dan wasan ya bayyana cewa zai ci gaba da tallafawa kungiyar.

Aubameyang – Na Fi Son Arsenal A Kan Barcelona

Suarez, mai shekara 33 a duniya ya kammala komawa kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ranar Juma’ar data gabata, kuma shi ne dan Barcelona na uku kan gaba a cin kwallaye a tarihi mai kwallaye 198 a raga a wasanni 283 a shekara shida da ya yi a Barcelona.

Dan wasan na Uruguay  ya zama na farko da ya ci wa Atletico kwallo biyu da fara wasansa, kuma na farko da ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga a karawar dan wasa ta farko a La Liga a kungiyar.

Bayan an tashi daga wasan kociyan kungiyar, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa ga dan wasan inda kuma ya bayyana cewa photo voltaic samu babban dan wasa kuma zai taimaka musu wajen ganin photo voltaic cike gurbin dake tsakaninsu da kungiyoyin Precise Madrid da Barcelona.

What's On Your Mind?