Soyayya da mai mata kamar tuwo ba miya ne saboda ba kiran tsakar dare, ba na sassafe sai in ya saci fita, in ji budurwa

0
16

Wata yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @ayeesh_chuchu ta bayyana cewa soyayya da namiji mai mata yana da tarin takura da tauye romon jin dadin soyayyar.

@ayeesh_chuchu ta bayyana cewa irin wannan soyayya tamkar gayar tuwo babu miya ne saboda mutum ba zai samu cikakken lokacin kasancewa tare da masoyin nasa ba sai dai idan ya yi nisa da iyalinsa.

Soyayya da mai mata kamar tuwo ba miya ne saboda ba kiran tsakar dare, ba na sassafe sai in ya saci fita, in ji budurwa

Ta ce a irin wannan soyayyar, mutum ba zai samu damar hira da masoyin nasa ta waya ba a tsakar dare da kuma sassafe. Sannan ta ce ko sakon tex mutum ba zai iya aikawa dangerous a tsakar dare.

Ta kuma bayyana cewa lokaci guda da mutum zai samu sararin kasance da shi shine idan baya tare da matarsa ta gida ko kuma idan ya fita yin wasu harkoki.

Ta ce: “Soyayya da mai mata na tattare da takura sosai wolla…Ehnn! babu wayan tsakar dare, babu kiran sassafe..Babu sakon tex na tsakar dare. Za ka kasance tare da shi ne kawai idan ya iya samun sarari daga iyalinsa ko kuma ya saci fita sannan ya hadu da ke. Gaya ne zalla kamar tuwo ba miya.”

Mobilized9ja ta tattaro wasu daga cikin martanin mabiya shafin a kasa:

An hallaka mutum 80 yayin rikicin ƙabilanci

@Bntabbas ta yi martani cewa

“Uzuri kamar; Zan je aski Bari in siyo Bread din protected, Zamu je ball, Zan karbo kayan wanki And so forth”

@salmah_farouk ta ce:

“Wow ta yaya kika san wadannan abubuwan? Kina da aure ne.”

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda solar cafke wadanda ake zargi 4, solar kwato shanu 200 da makamai a Zamfara

@Burhan_muksamad

“Hmn. Hakan na nufin ya san darajar matarshi ne, yake bata lokaci, kema ya baki naki daban, da ace baisan darajar matarshi ba, da waya zai dnga yi a gabanta dake. Imma ya kasance miji nagari ko kuma wanda matarsa ke juya shi.”

@_Maymunatuu ta ce:

“Wllh ko haka ne. Amma sunfi sanin darajar Ki.”

@jimada_ibm ya ce:

“Idan ke kika tsinci kanki a matsayin matar namiji mai aure, zaki so mijinki ya aikata wadannan abubuwan da kika ambata da macen da bai riga ya aura ba? Ki kara hakuri, idan ya auree ki, za ku samu lokacin da kuke bukata a tare cikin kwanciyar hankali bisa halali.”

A wani labarin, wata matashiyar yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @Mareeyarhh ta shawarci mata a kan su guji auren mazan Hausawa idan har suna son kwanciyar hankali a gidan aurensu.

Matashiyar budurwar bata tsaya a nan ba, ta kuma shawarci mata a kan su guji auren Mazan hausawa da suka fito daga Kano idan har suna son jin dadin aure.

Mutane da dama solar yi martani a wallafar da matashiyar tayi yayinda wasu da dama musamman maza suka caccake ta.

What's On Your Mind?